Gabanin tasowa daga kasar UAE, Buhari ya gana da Yariman Abu Dhabi (Hotuna)

Gabanin tasowa daga kasar UAE, Buhari ya gana da Yariman Abu Dhabi (Hotuna)

Gabanin tashin jirgin shugaba Muhammadu Buhari daga kasar UAE inda ya je halartan taron sanya hannun jari, ya gana da Yariman birnin Abu Dhabi, kan harkokin Diflomasiyya tsakanin Najeriya da kasar UAE.

Shugaba Buhari ya gana Yarima mai jiran gado, Mohammed Bin Zayed Al Nahyan, a ranar Talata, 9 ga watan Afrilu, 2019.

Gabanin tasowa daga kasar UAE, Buhari ya gana da Yariman Abu Dhabi (Hotuna)

Gabanin tasowa daga kasar UAE
Source: Facebook

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da kungiyoyi 6 na masu saka hannun jari bayan kammala taron masu saka hannun jari na wannan shekara da aka yi a Dubai.

A jawabin da Femi Adesina, kakakin shugaban kasa ya fitar, Buhari ya aika sako daya ga masu saka hannun jarin: "Ku zo Najeriya domin samun riba a kasuwancinku cikin kankanin lokaci."

Gabanin tasowa daga kasar UAE, Buhari ya gana da Yariman Abu Dhabi (Hotuna)

Gabanin tasowa daga kasar UAE, Buhari ya gana da Yariman Abu Dhabi (Hotuna)
Source: Facebook

Sheikh Ahmed Al Maktoum, dan cikin gidan sarautar kasar Dubai kuma daya daga cikin masu saka hannu jari, ya nuna sha'awarsa ta kafa cibiyar samar da hasken wutar lantarki a Legas.

Mista Yusuff Ali, shugaban kamfanin 'Lulu Group' masu manyan shagunan kayan sayar wa a yankin gabsa ta tsakiya da Asia, ya nuna sha'awarsa ta hada gwuiwa da manoma a Najeriya domin samun kayan amfanin gona masu inganci da tsafta. Rukunin shagunan 'Lulu' na da ma'aikata fiye da 50,000.

Gabanin tasowa daga kasar UAE, Buhari ya gana da Yariman Abu Dhabi (Hotuna)

Gabanin tasowa daga kasar UAE, Buhari ya gana da Yariman Abu Dhabi (Hotuna)
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel