'Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 3,000 a Zamfara - Gwamna Yari

'Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 3,000 a Zamfara - Gwamna Yari

Abdulaziz Yari, gwamnan jihar Zamfara, ya bayyana cewar 'yan bindiga sun kashe mutane 3,526 a jihar Zamfara a ckin shekaru biyar da suka gabata.

Yari ya bayyana hakan ne a wurin wani taro da aka yi a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, a ranar Talata.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar shugaban rundunar 'yan sanda na kasa (IGP), Mohammed Adamu, sarakunan gargajiya, shugabannin manoma da na makiyaya sun halarci taron

Yari, wanda sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Abdullahi Shinkafi, ya wakilta, ya ce 'yan bindigar sun lalata kusan kauyuka 500.

Ya kara da cewa, "sun lalata fiye da hekta 13,000 na gonaki, yanzu manoma basu da gonakin da zasu yi noma.

'Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 3,000 a Zamfara - Gwamna Yari

Abdulaziz Yari
Source: Depositphotos

"Sun lalata kauyuka kusan 500, sun raunata mutane 8,219, wasu daga cikinsu suna ciin mawuyacin hali har yanzu.

"Tattalin arzikin jiha ya samu babban nakasu aboda dubban shaguna da 'yan bindigar suka lalata tare da raba dubban jama'a da gidajensu, da yawan mutane basa iya bacci da idanuwansu biyu a rufe saboda tsoro."

Yari ya ce gwamnatinsa ta rubuta rahotanni da shafinsu ya haura 7,000 a kan rigingimun jihar tun farkon shigowar baki daga Libya da kuma mambobin Boko Haram.

DUBA WANNAN: Hanyar lafiya: Abubuwa 10 da ya kamata ku kiyaye lokacin zafi

Ya ce gwamnati na da masaniya a kan fitattun sansanin 'yan ta'adda 8 da ke sassan jihar.

Gwamnan ya kara da cewa akwai bukatar a kara daukan matakin tabbatar da zaman lafiya a jihar bayan dakatar da harkokin hakar ma'adanai.

A jawabinsa, IGP Adamu ya shaida wa mahalarta taron cewar rundunar 'yan sanda za ta dauki matakan kare jama'a daga hare-haren 'yan bindigar, sannan ya yaba wa gwamnatin jihar bisa samar da kyakyawan yanayi domin jami'an tsaro su gudanar da aikinsu.

Ko a cikin satin da ya gabata sai da rahotanni suka bayyana cewar an kashe mutane 50, da suka hada da 'yan sa kai (CJTF), a Kauran Namoda a cikin rana guda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel