Yan Najeriya 446 ke tsare a kurkukun kasar Dubai - Jakada

Yan Najeriya 446 ke tsare a kurkukun kasar Dubai - Jakada

Jimillan yan Najeriya 446 suke tsare a gidan yarin kasar UAE (Dubai), yankin Larabawa, Jakadan Najeriya, Mohammad Dansanta Rimi ya bayyana hakan ranar Litinin, 9 ga watan Afrilu, 2019.

Rimi, ya bayyana hakan ga shugaba Muhammadu Buhari wanda ya kai ziyara kasar yayinda yake ganawa da yan Najeriya mazauna kasar UAE da rana kafin tawowarsa Najeriya.

Ya ce yan Najeriya 446 ke tsare a kasar sakamkon safarar muggan kwayoyi da wasu laifuka.

Jakadan ya laburta wannan makonni bayan an damke yan Najeriya biyar da aka kama da laifin fashi da makami a Dubai.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Hukumar sojin Najeriya sun ragargarji yan Boko Haram a Damaturu da daren nan

A wani labarin, Bayan kwanaki hudu kacal da tsayarwa wata yar Najeriya haddin kisan kai sakamakon safarar muggan kwayoyi, an sake kama wani dan Najeriya mai suna, Saheed Sobade, da Gram 1,183 na hodar Iblis a birnin Jiddah, kasar Saudiyya.

Babbar hadimar shugaban kasa kan harkokin wajen Najeriya, Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana hakan ne ranar Juma'a yayin hira a tashar Arise TV.

Tace: "Akwai wani labarin takaici da zan baku. Jiyan nan, ana cikin tunani kan yan Najeriya 20 da za'a tsayarwa haddi, bayan takwas da aka yankewa, an kama wani dan Najeriya da hodar Iblis."

"An kamashi da giram 1,183 na hodar Iblis. Ana kamashi aka sanar da ofishin jakadanci kuma sunarsa, Saheed Ayinde Sobade."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel