INEC ta tsayar da lokacin gudanar da zaben gwamna a Kogi da Bayelsa

INEC ta tsayar da lokacin gudanar da zaben gwamna a Kogi da Bayelsa

Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta tsayar da ranar 2 ga watan Nuwamba domin gudanar da zaben gwamna a jihohin Bayelsa da Kogi.

Hukumar zaben ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na tuwita.

A cikin takardar sanarwar, INEC ta ce; "bayan tattaunawar da muka yi a yau (Talata), mun amice da fitar da jadawalin harkokin zabe a jihohin Bayelsa da Kogi, wanda za a gudanar da zabe a ranar 2 ga watan Nuwamba, 2019.

"Mun ware ranakun 2 ga watan Agusta zuwa 29 domin bawa jam'iyuun da ke da sha'awar tsayar da 'yan takara a zabukan jihohin damar gudanar da zaben fidda 'yan takara.

INEC ta tsayar da lokacin gudanar da zaben gwamna a Kogi da Bayelsa

Farfesa Mahmoud Yakubu; shugaban hukumar INEC
Source: UGC

"Jam'iyyu zasu fara yakin neman zabe daga ranar 2 ga watan Agusta sannan a rufe a ranar 31 ga watan Oktoba na shekarar 2019.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya bar Dubai, an yi masa bikin bankwana (Bidiyo)

"Za a rufe karbar sunayen wakilan jam'iyyu ga duk jam'iyyar da ta tsayar da dan takara, a ranar 2 ga watan Oktoba."

INEC ta kara da cewa duk mai neman karin bayani a kan ragowar harkokin da suka shafi zaben gwamna a jihohin, zai iya garzaya wa ya zuwa shafinsu na yanar gizo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel