Da duminsa: Rundunar soji ta yi arangama da mayakan Boko Haram kan hanyar Damaturu-Maiduguri

Da duminsa: Rundunar soji ta yi arangama da mayakan Boko Haram kan hanyar Damaturu-Maiduguri

Rahotanni daga gidan talabijin na TVC na nuni da cewa a yanzu haka dakarun rundunar soji na musayar wuta da mayakan Boko Haram kan hanyar Damaturu-Maiduguri.

Rahotanni sun bayyana cewa mazauna yankin da ake musayar wutar sun shiga gidajensu tare da garkamewa domin gudun kisan wanda bai ji ba bai gani ba.

KARANTA WANNAN: Zargin aringizon kuri'u: Kotu ta amince da bukatar PDP na binciken kayayyakin zaben Kano

Haka zalika rahotanni sun bayyana cewa an ga jiragen yakin rundunar soji na sama da ke luguden wuta kan mayakan Boko Haram.

Cikakken labarin yana zuwa...

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel