Zargin aringizon kuri'u: Kotu ta amince da bukatar PDP na binciken kayayyakin zaben Kano

Zargin aringizon kuri'u: Kotu ta amince da bukatar PDP na binciken kayayyakin zaben Kano

- Kotu ta amince da bukatar PDP na binciken kayayyakin da INEC ta yi amfani da su wajen gudanar da zaben gwamnan jihar

- Alhaji Abba Kabiru Yusuf na kalubalantar nasarar da hukumar zaben ta ce gwamna Abdullahi Ganduje ya samu a zaben gwamnan jihar na ranar 23 ga watan Maris

-Rahotannin sun bayyana cewa PDP na da kwanaki biyar ta shigar da APC kara kotu bayan cinye kwanaki 15 cikin 21 da dokar zaben kasar ta 2010 ta tanar

Kotun da ke sauraron korafe korafe kan zaben gwamnan jihar Kano ta amince da bukatar jam'iyyar PDP na binciken kayayyakin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yi amfani da su wajen gudanar da zaben gwamnan jihar.

Dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar PDP Alhaji Abba Kabiru Yusuf na kalubalantar nasarar da hukumar zaben ta ce gwamna Abdullahi Ganduje na jam'iyyar APC ya samu a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 23 ga watan Maris.

A cikin wata takardar korafi da ya gabatar gaban kotun, wacce ke karkashin mai shari'a Halima Shamaki, lauyan dan takarar PDP, Maliki Kuliya-Umar ya bukacin kotun da ta umurci INEC ta baiwa jam'iyyar kayayyakin da aka gudanar da zaben da su a ranar 9 ga watan Maris da kuma 23 ga watan Maris domin ta yi bincike kan su.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Yan ta'adda da jami'an sa kai sun fafata a Katsina, 14 sun mutu

Zargin aringizon kuri'u: Kotu ta amince da bukatar PDP na binciken kayayyakin zaben Kano

Zargin aringizon kuri'u: Kotu ta amince da bukatar PDP na binciken kayayyakin zaben Kano
Source: Twitter

Mai shari'a Shamaki ta umurci INEC da ta baiwa jam'iyyar dukkanin kayayyakin zaben da ta yi amfani da su wajen gudanar da zaben Kano, bisa ga dalilan da jam'iyyar ta bayar na son binciken kayayyakin.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa jam'iyyar PDP na da kwanaki biyar ta shigar da APC kara kotu bayan da ta cinye kwanaki 15 cikin 21 da dokar zaben kasar ta 2010 ta tanar kamar yadda aka sabunta.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel