Tsohon gwamna Jang ya karkatar da N2bn na kananan sana’o’i - Shaida

Tsohon gwamna Jang ya karkatar da N2bn na kananan sana’o’i - Shaida

Wani idon shaida, Mista Taiwo Olorunyomi, mai bincike a hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC yayi zargin cewa Gwamna Jonah Jang ya karkatar da naira biliyan 2, wanda babban bankin kasa (CBN) ta saki ga gwamnatin jihar don kananan sana’o’i.

NAN ta ruwaito cewa a ranar 7 ga watan Mayu, EFCC ta gabatar da tuhume-tuhume 12 na cin hanci akan Jang.

Anyi zargin cewa Jang, wanda yayi aiki a matsayin gwamnan jihar Plateau tsakanin 2007 da 2015, yayi wadaka da naira biliyan shida, watanni biyu kafin saukarsa daga kujerar gwamna.

Da ake gabatar da hujjoji karkashin jagoranxin RotImi Jacob (SAN) lauyan ICPC, a wata babbar kotu da ke Plateau, Olorunyomi yace: “CBN ta shiga yarjejeniyar hadin gwiwa da gwamnatin Plateau domin samar da wani hukumar ci gaba na kananan sana’o’in jiha wanda za a rarraba kudade sannan a dawo da su.

NAN ta ruwaito cewa EFCC tayi zargin cewa Jang ya handame kudin ta hannun Mista Pam Yusuf, wani kashiya a wancan lokacin na ofishin sakataren gwamnatin jiha.

Tsohon gwamna Jang ya karkatar da N2bn na kananan sana’o’i - Shaida

Tsohon gwamna Jang ya karkatar da N2bn na kananan sana’o’i - Shaida
Source: UGC

Olorunyomi ya kuma yi ikirarin cewa wanda ake tuhuman ya kuma zari wasu zunzurutun kudi har naira biliyan 300, naira miliyan 700 da kuma naira miliyan 400 daga asusun SUBEB na jihar.

Ya bayyana cewa Jang yace an ranci kudin ne daga asusun don biyan masu aikin kwangila, da sauransu a jihar.

Idon shaidan ya bayyana cewa Pam ya cire kudin sannan ya gabatar dashi ga Jang inda ya bayyana cewa ayyukansu ya taushe gudanarwar SUBEB a lokacin da yake gwamnan jihar.

Har ila yau, Jacob yayinda yake gabatar da shaida na biyu, sakataren gwamnatin jihar Plateau, ya roki kotu da ta amince da takardun da shaidan ya gabatar.

Lauyan Jang, Mike Ozekhome (SAN), ya ki amincewa da rokon, inda ya bayyana cewa mai karan bai gabatar masa da takardu ba kafin zaman don haka ba zai iya gabatar da makamancin hakan ba a kotu, inda ya bayyana hakan a matsayin ‘bazata’.

Ozakhome ya roki kotu da ta yi watsi da kiran shaidan sannan ta amince da jawabin wanda ake tuhumaa na biyu domin ba a bashi takardu ba kafin zaman kotun.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Babbar birnin jihar Yobe, Damaturi na karkashin harin Boko Haram

Alkalin, Justis Daniel Longji, da yake zartar da hukunci, ya bayyana cewa bai kamata wani bangare ya shammaci wani ba musamman a shari’a na wani laifi.

Longji ya bayyana cewa idan har sai an gabatar da wata takarda a matsayin shaida, ya zama dole wanda ake tuhuman ma ya mallaki takardan.

Ya dage sauraron shari’an zuwa ranar 11 ga watan Afrilu, domin ci gaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel