Cin hanci: ICPC ta cafke shugabanin Polytecnic na tarayya guda uku

Cin hanci: ICPC ta cafke shugabanin Polytecnic na tarayya guda uku

- An kama shugabanin Kwallejojin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya guda uku da laifin karkatar da kudi

- Wadanda aka kama sun hada da Abubakar Sadiq Yahaya na Federal Polytechnic Mubi, John Taiwo Adekolawole, Federal Polytechnic, Ede a jihar Osun sai Arch. Waziri Sanusi Gumau na Federal Polytechnic da ke jihar Bauchi

- An kama su ne dauke da N10,250,000 a wata sumame da aka kai a harabar Cibiyar Ilimin Fasaha (NABTE) a Abuja bayan wani ya tseguntawa ICPC abinda suke shirin yi

Badakallar N10.2m: ICPC ta cafke shugabanin Polytecnic guda uku

Badakallar N10.2m: ICPC ta cafke shugabanin Polytecnic guda uku
Source: UGC

Hukumar yaki da rashawa, ICPC ta kama shugaba da manyan mambobin kwamitin shugabanin Kwallejin Kimiyya da Fasaha na Tarayya (COFER) uku da ake zargi da karbar cin hanci na zunzurutun kudi Naira Miliyan 10.2.

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta kori manyan jami'an ta 9 saboda saba dokar aiki

Wadanda aka kama sune; Abubakar Sadiq Yahaya, Kwallejin Kimiyya da Fasaha da ke Mubi, Jihar Adamawa, wanda kuma shine shugaban COFER; John Taiwo Adekolawole, Kwallejin Kimiyya da Fasaha da ke Ede a jihar Osun; Arch. Waziri Sanusi Gumau na Kwallejin Kimiyya da Fasaha na Tarayya da ke Bauchi, a jihar Bauchi.

Sanarwar da Kakakin ICPC, Rasheedat Okoduwa ta fitar a ranar Talata ya tabbatar da cewa an kama su ne a wata sumame da ICPC ta kai a harabar Cibiyar Ilimin Fasaha (NABTE) a Abuja.

Wadanda aka kama tare da shugabanin Kwallejin Fasaha's har da sakataren COFER, Ayegba Benjamin Godwin dauke da tsabar kudi N10,250,000 bayan wani dan tonon asiri ya sanar da ICPC cewa mutane hudun da wasu suna shirin karya dokar rashawa na 2000.

Za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike duk da cewa a halin yanzu an bayar da belinsu kamar yadda Okoduwa ta bayyana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel