Akwai sarakuna da ke hada baki da 'yan bindiga a Zamfara - Ministan tsaro

Akwai sarakuna da ke hada baki da 'yan bindiga a Zamfara - Ministan tsaro

Mansur Dan-Ali, ministan tsaro, ya yi zargin cewar akwai wasu masu rike da sarautar gargajiya da ke bayar da muhimman bayanai ga 'yan bindigar jihar Zamfara.

A jawabin da kakakinsa, Tukur Gusau, ya fitar amadadinsa, Dan-Ali ya ce da dama daga cikin 'yan bindigar da suka addabi jihar sun mutu biyo bayan luguden wuta da dakarun sojin sama suka yi a wasu sanannun maboyar 'yan ta'addar, lamarin da ya kai ga kubutar da mutane da yawa.

Ya ce gwamnatin tarayya ta damu matuka da tabarbarewa tsaro a jihohin arewa maso yamma, musamman a Zamfara, Sokoto, Katsina da Birnin Gwari a jihar Kaduna.

"Dakarun sojin sama sun matsa da kai hari a kan 'yan bindigar Zamfara. An kashe da dama daga cikin 'yan bindigar tare da kubutar da jama'a da dama.

Akwai sarakuna da ke hada baki da 'yan bindiga a Zamfara - Ministan tsaro

Ministan tsaro; Mansur Dan Ali
Source: UGC

"Gwamnatin tarayya na iya bakin kokarinta wajen gano silar aiyukan ta'addanci da 'yan bindiga ke yi a jihar Zamfara.

"Gwamnatin tarayya ta dakatar da aiyukan hakar gwal a jihar Zamfara biyo bayan shawarar da ministan tsaro ya bayar na bukatar a yi hakan saboda alakar da ke tsakanin aiyukan ta'addanci da hakar ma'adanai a jihar.

DUBA WANNAN: Zanga-zanga: 'Yan sanda sun harba wa ma'aikatan INEC na wucin gadi barkonon tsohuwa

"Ya kamata jama'a su sani cewar batun ta'addanci abu ne dake damun duk duniya, kuma ba za a iya magance shi ta hanyar amfani da karfin soji ba kadai. Dole jama'a su tashi tsaye domin bawa gwamnati goyon baya wajen magance wannan matsala.

"Amma duk da wannan kokari da gwamnati ke yi, akwai wasu marasa kishi da suka hada da manyan sarakunan gargajiya da ke hada baki tare da taimakon 'yan ta'adda da muhimman bayanan sirri domin su samu damar aikata ta'addanci ko cin dunduniyar yunkurin dakarun soji," a cewar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel