Wadanda suka yi garkuwa da Shugaban sashin kashe gobara na Lagas, sun bukaci kudin fansa

Wadanda suka yi garkuwa da Shugaban sashin kashe gobara na Lagas, sun bukaci kudin fansa

Wadanda suka yi garkuwa da Shugaban sashin kasha gobara na jihar Lagas, Rasaki Musibau, da wasu mutane shida sun kira iyalansu domin neman kudin fansa.

An tattaro cewa masu garkuwan na neman naira miliyan shida a matsayin kudin fansar sakin Mista Misbau yayinda aka nemi kasa da hakan daga iyalan sauran wadanda aka yi garkuwa da su.

A bisa ga rahoton da ya billo, masu garkuwan sun sha alwashin kin karban kasa da naira miliyan uku daga iyalan Musibau.

Kakakin yan sandan jihar Lagas, Bala Elkana, da yake Magana kan lamarin ya bayyana cewa rundunar za ta yi duk abunda ya kamata don ceto mutanen.

Wadanda suka yi garkuwa da Shugaban sashin kashe gobara na Lagas, sun bukaci kudin fansa

Wadanda suka yi garkuwa da Shugaban sashin kashe gobara na Lagas, sun bukaci kudin fansa
Source: UGC

Anyi garkuwa da Mista Rasaki Musibau da wasu shida a hanyar Epe-Itokin, Ikorodu a karshen makon.

KU KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun gurfanar da mutune 3 da aka kama suna yunkurin tono gawa daga kabari

Masu garkuwan sun sace su ne zuwa wani wuri da ba a sani ba.

An tattaro cewa sun toshe hanyar gadar Itokin, inda suka kai harin bazata ga wasu mutane a motocin Sienna, Corolla da kuma wata motar SUV.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Babban sufetan Yansandan Najeriya, Muhammed Adamu ya kai ziyarar gani da ido jahar Zamfara don gane ma idanunsa irin wainar da ake toyawa a jahar biyo bayan sake ruruwan matsalar tsaro data dangancin ayyukan yan bindiga a jahar.

An ruwaito IG Adamu ya isa Gusau, babban birnin jahar Zamfara ne da misalin karfe 3 na rana, inda kai tsaya ya wuce taron masu ruwa da tsaki da rundunar Yansandan jahar ta shirya da al’ummar jahar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel