Aiki ga mai kareka: Babban sufetan Yansanda ya garzaya jahar Zamfara don ganin wainar da ake toyawa

Aiki ga mai kareka: Babban sufetan Yansanda ya garzaya jahar Zamfara don ganin wainar da ake toyawa

Babban sufetan Yansandan Najeriya, Muhammed Adamu ya kai ziyarar gani da ido jahar Zamfara don gane ma idanunsa irin wainar da ake toyawa a jahar biyo bayan sake ruruwan matsalar tsaro data dangancin ayyukan yan bindiga a jahar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito IG Adamu ya isa Gusau, babban birnin jahar Zamfara ne da misalin karfe 3 na rana, inda kai tsaya ya wuce taron masu ruwa da tsaki da rundunar Yansandan jahar ta shirya da al’ummar jahar.

KU KARANTA: Gobara ta tafka mummunan barna a jami’ar Umaru Musa Yar’adua

A jawabinsa, IG Adamu yace makasudin ziyarar daya kawo shine tabbatar da an bi umarnin gwamnatin tarayya na dakatar da duk wasu ayyukan hakar ma’adanan kasa a jahar Zamfara gaba daya.

Hakanan abu na biyu daya kawo shi jahar Zamfara shine jin ta bakin shuwagabannin gargajiya, shuwagabannin addinai, manoma, makiyaya da da sauran jama’a game da matsalar yan bindiga data addabi jahar.

Daga nan IG ya nemi goyon bayan masu ruwa da tsaki a jahar Zamfara ta wajen bayar da bayanan sirri ga hukumomin tsaro ta yadda zasu kawo karshen ayyukan miyagu a jahar, tare da tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma.

Sai dai a nasa jawabin, shugaban karamar hukumar Zurmi ta jahar Zamfara, Auwal Bawa ya nemi babban sufetan daya hada kai da Sojoji sa kai watau civilian JTF wajen yaki da yan bindiga a jahar, don haka ya nemi rundunar Yansanda da taimaka ma Sojojin sa kai da makamai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel