Shugaba Buhari ya yi magana kan kashe-kashen jihar Kaduna

Shugaba Buhari ya yi magana kan kashe-kashen jihar Kaduna

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tirr da kashe-kashen da ya auku a jihar Kaduna inda aka ruwaito cewa akalla mutane 20 sun rasa rayukansu a garin Adara dake karamar hukumar Kajuru.

Wannan rikicin takaicin yana kara zurfafa kiyayya tsakanin yan kabilan Adara da yan Fulani dake yankin, wadanda suka dade suna rashin jituwa tsakaninsu.

Shugaban kasa, ta bakin mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya yi tirr da wannan inda hada da tsokaci kan kashe-kashe kungiyoyin daba a jihar Ribas.

Ya yi kira zaman lafiya da kuma daina ramuwar gayya saboda wannan dabi'a kan kara janyo yawan hare-hare tsakanin kabilun gud biyu inda mutane da dama suke rasa rayukansu a karamar hukumar Kajuru da Kachia dake jihar Kaduna.

KU KARANTA: Gwamnan Anambra ya kawo karshen rikicin makiyaya da manoma a jihar

Shugaba Buhari ya yi kira da mazauna Kaduna da sauran yan Najeriya da su daina maganganu da ka iya tayar da tarzoma a kafofin ra'ayi da sada zumunta musamman wadanda basu san tarihi ba.

Irin wadannan maganganu ka iya tayar da kura tsakanin al'ummomi guda biyu.

Hakazalika shugaba Buhari ya yi kira ga sarakunan gargajiya da malaman addini su yi takatsantsan wajen furta kalamai kan rikice-rikice. Ya ce duk maganan da zasuyi ya kasance na hada kai da zaman lafiya.

Mun kawo muku rahoton cewa A kalla mutane 20 ne rahotanni suka bayyana an kashe a sabon harin da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai kauyen Angwan Aku dake karkashin karamar hukumar Kajuru a jhar Kaduna.

Wani cikin mazauna garin ya shaida wa majiyar mu cewar, 'yan bindigar bindiga cikin kayan soji da bindigu samfurin AK47 da wukake da sanduna sun kai harin da misalin karfe 7:00 na daren Litinin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel