Juventus za ta doke Barcelona a wasan karshe na cin kofin UCL na Turai

Juventus za ta doke Barcelona a wasan karshe na cin kofin UCL na Turai

Ana tunani Juventus ne za su lashe gasar cin kofin kwallon kafa na Nahiyar Turai watau UCL na shekarar bana. Hakan na zuwa ne bayan wata na’ura ta cinko cewa kungiyar ta kasar Italiya tayi nasara.

Hasashen wata babbar na’ura ya nuna cewa Juventus za ta doke kungiyar Barcelona a wasan karshe na babban gasar da za a buga a wannan shekarar. Za a doka wasan karshe ne a Ranar 1 ga Watan Yunin 2019 a Birnin Madrid na Sifen.

Yanzu haka dai Juventus za su tafi kasar Holand inda za su kara da kungiyar Ajax a filin wasa na Amsterdam Arena. Juventus za su fafata ne a wasan farko na karon na kusa da daf-da wasan karshe, a cikin tsakiyar wannan makon.

Kungiyar Barcelona kuma za ta fafata ne da Manchester United a wannan rukuni. Idan wadannan kungiyoyi sun samu nasara, akwai yiwuwar su hadu a zagayen karshe inda wannan na’ura ta ke ganin Barcelona ce za ta rasa kofin.

KU KARANTA: Abubuwan da za su sa ‘Dan wasa Neymar ya tattara ya bar PSG

Tun a kakar 1995-96 da Juventus ta ci kofin na Turai, ba ta sake samun nasara ba har gobe. A 2017 ne Juventus da Barcelona su ka kara da juna inda aka lallasa Juve. Barcelona ta casa kulob din na Italiya ne da ci 3-0 a shekarar.

Sportskeeda tace Zakarun na Sifen da Italiya watau Barcelona da Juventus ne za su kai wasan karshe inda a karshe Juventus za tayi nasara. A kakar bara ne dai kungiyar Juventus ta saye fitaccen ‘Dan wasa Cristiano Ronaldo.

A 2015 ne Barcelona ta daga kofin na Champions League bayan ta lallasa Juventus da ci 3-1. A makon jiya ne Juventus ta bada mamaki a wasan ta da Atletico Madrid inda Cristiano Ronaldo ya ci kwallaye 3 a zagaye na biyu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng News

Online view pixel