Zanga-zanga: 'Yan sanda sun harba wa ma'aikatan INEC na wucin gadi barkonon tsohuwa

Zanga-zanga: 'Yan sanda sun harba wa ma'aikatan INEC na wucin gadi barkonon tsohuwa

Jami'an 'yan sanda a jihar Enugu sun yi amfani da barkonon tsohuwa a kan ma'aikatan wucin gadi na hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) a yayin da suke zanga-zangar rashin biyansu kudin aikin zabukan da suka yi a jihar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar barkonon tsohuwar da 'yan sandan suka harba, ya shafi masu wuce wa, da suka hada da dalibai da masu ababen hawa, lamarin da ya sa su gudun neman tsira.

Masu zanga-zangar da suka hada da matasa 'yan bautar kasa, dalibai da ma'aikata sun mamaye hedikwatar INEC a jihar tare da hana shiga ko fita daga ginin da ofishin ya ke.

Mista Tony Ani, mai shekaru 42, da ya yi aiki a matsayin mataimakin 'presidin officer (APO 3)' ya bayyana rashin jin dadinsa bisa wulakanta su da INEC ta yi da kuma rashin biyansu alawus-alawus dinsu na aikin zaben shugaban kasa da gwamnoni da suka yi a jihar.

Zanga-zanga: 'Yan sanda sun harba wa ma'aikatan INEC na wucin gadi barkonon tsohuwa

'Yan sanda sun harba wa ma'aikatan INEC na wucin gadi barkonon tsohuwa
Source: UGC

Wata 'yar bautar kasa, Chioma Emmanuel, ta ce ba a biya ta ko sisi ba har yanzu duk da tayi aiki a zaben shugaban kasa da na gwamnoni, ta ce hatta kudin bayar da horo ba a biya ta ba.

Ta ce sun yanke shawarar yin zanga-zanga ne bayan sun hada kansu a dandalin sada zumunta na Whatsapp.

DUBA WANNAN: Katsina:Gobara ta tafka barna a jami'ar UMYU

Da yake magana da manema labarai a kan zanga-zangar, kwamishinan INEC a jihar Enugu, Dakta Emeka Ononamadu, ya ce wasu ne suka dauki nauyin matasan domin tilastsa INEC biyansu kudi bayan basu yi aikin komai ba.

Onanamadu ya ki gabatar da jawabi ga masu zanga-zangar, sai dai, ya shaida wa manema labarai cewar masu zanga-zangar na daga cikin wadanda za a biya a rukuni na uku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel