Bamu ga ta zama ba har sai an kama masu wannan laifi -Tambuwal ya yi tsokaci kan dalibin da aka guntulewa hannu

Bamu ga ta zama ba har sai an kama masu wannan laifi -Tambuwal ya yi tsokaci kan dalibin da aka guntulewa hannu

Gwamna Aminu tambuwal na Sokoto ya bayyana cewa dukkanin shirye shirye na nan domin ganin cewa a kama wadanda suka yanke hannuwan dalibin jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto mai suna Habibu Abubakar Nakasari, dalibin wanda ke aji biyu kuma yana karantar turanci.

Majiyar Legit.ng tace Tambuwal yayi wannan furucin ne yayin day a ziyarci wannan dalibin a Asibitin kasha dake Wamakko idan aka kwantar da shi.

Zamu kama masu wannan laifin, inji Tambuwal

Habibu Nakasari
Source: UGC

KU KARANTA:Katsina:Gobara ta tafka barna a jami'ar UMYU

Da yake Magana a wajen, mataimakin Gwamnan Maniru Muhammad Dan’iya wanda ya wakilici maigidansa yace: “Gwamna wa umurceni da inzo in duba ka da kuma iyalanka kana kuma in sanar daku cewa gwamnatinmu ta dukufa akan aiki don ganin cewa a kama masu wannan laifi an kuma gabatar dasu gaban shari’a.”

Ya sake jaddadawa: “Wannan mummunan aiki ya fara zama abin yi musamman tsakanin matasa wanda Gwamnatinmu ba zata amince dashi ba kuma wannan shi zai kasance tamkarsa na karshe a wannan Jihar in Allah Ya yarda.”

Dan’iya ya fadi cewa Gwamna Tambuwal ya bada umurnin cewa Gwamnatinsa ce zata dauki nauyi kudi asibitin daku magunguna. A karshe kuma yayi addu’ar samun nasar cafke wanda sukayi wannan aika aika bada dadewa ba

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel