Jami'ar UDUS za ta karrama Dangote da wasu Sarakunan Arewa biyu

Jami'ar UDUS za ta karrama Dangote da wasu Sarakunan Arewa biyu

Jami'ar Usmanu Danfodio da ke Sokoto (UDUS) za ta bawa wasu manyan 'yan Najeriya uku da digirin Dakta na karramawa.

Wadanda aka karrama sune; Sarkin Gwandu Alhaji Muhammad Ilyasu Bashar, Alhaji Aliko Dangote da Sheikh Muhammad Mujtaba Isah Talata Mafara.

Shugaban jami'ar ta UDUS, Farfesa Abdullahi Abdu Zuru ne ya bayyana hakan a ranar Talata a wurin taron jajibirin yayen daliban jami'ar inda ya ce za a bayar da digirin karramawar ne a ranar 13 ga watan Afrilun 2019.

DUBA WANNAN: Saurayi ya kashe wacce zai aura saboda ta raina girman mazakutarsa

Jami'ar UDUS ta karrama Dangote da wasu Sarakuna biyu

Jami'ar UDUS ta karrama Dangote da wasu Sarakuna biyu
Source: Getty Images

Ya ce sun taka rawar gani a bangarorin rayuwarsu kuma sun bayar da muhimmin gudunmawa wurin inganta ilimi a Najeriya.

Farfesa Zuru ya kuma ce jami'iyyar za ta kuma karrama tsaffin ma'aikatan ta da su kayi murabus, Mai martaba Sarkin Yauri, Dr Mohammed Zayyanu Abdullahi da Ambasada Farfesa Tijjani Bande.

Ya bayyana cewa mutane biyun sun sadaukar da rayuwarsu wurin yiwa UDUS da kasarsu hidima.

"Za a karrama su da digiri ta Emeriti wanda hakan zai sanya su kasance tare da jami'an har abada," inji shi.

Ya yi bayanin cewa za a karrama Sarkin Yauri da 'Vice Chancellor Emeritus' shi kuma Farfesa Bande za a karrama shi da 'Professor Emeritus'.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel