Gwamnan Anambra ya kawo karshen rikicin makiyaya da manoma a jihar

Gwamnan Anambra ya kawo karshen rikicin makiyaya da manoma a jihar

- A karshe dai gwamnan jihar Anambra Willie Obiano ya kawo karshen rikicin da ke tsakanin manoma da makiyaya a jihar

- Jihar Anambra ta na samun rikice-rikice na makiyaya da manoma a jihar, musamman a kauyukan da ke makwabtaka da wasu jihohin

Gwamnatin jihar Anambra ta tabbatar da cewa ta kawo karshen rikicin da ke tsakanin makiyaya da manoma da ke garin Anam a karamar hukumar Anambra ta yamma da ke jihar.

Rahotanni sun nu na cewa an kashe wasu mutane sannan an jiwa wasu munanan raunuka a wasu gonaki guda biyu da ke garin Anam, bayan wani sabon hari da makiyayan suka kai gonakin na su.

Mista Don Adinuba, kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama'a na jihar ya bayyana cewa rikicin ya zo karshe a yankin.

Gwamnan Anambra ya kawo karshen rikicin makiyaya da manoma a jihar

Gwamnan Anambra ya kawo karshen rikicin makiyaya da manoma a jihar
Source: Depositphotos

Ya ce an samu damar kawo karshen rikicin bayan da gwamnan jihar Willie Obiano ya bukaci hukumomin tsaro na jihar da su gaggauta kawo karshen rikicin.

Sannan ya kara da cewa bayan haka kuma an bawa jami'an tsaron su binciko ainahin dalilin da ya kawo rikicin, domin gujewa irin rikicin a nan gaba.

KU KARANTA: Jerin Ministocin da shugaba Buhari zai koma mulki da su

Jami'an tsaron sun gano cewa rikicin ya samo asali ne ta dalilin shigowar wasu makiyaya da suke zaune a jihohin da suke makwabtaka da jihar, inda suke shigowa ta hanyar da bata dace ba.

A karshe Adinuba ya bai wa mutanen da abin ya shafa hakuri, sannan kuma ya yi musu alkawarin cewa gwamnati baza ta bar wasu tsirarun mutane su dinga zuwa suna ta da hankalin al'umma ba. Saboda haka gwamnati za ta yi iya bakin kokarin ta wurin kawo karshen duk wani rikici a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel