Katsina:Gobara ta tafka barna a jami'ar UMYU

Katsina:Gobara ta tafka barna a jami'ar UMYU

- Wata gobara ta tafka barna a ginin ofisoshin malamai da wasu tsangayun karatu a jami'ar Umaru Musa Yar'adu

- Wasu da suka je kallon gobarar sun bayyana cewar suna zargin cewar wutar lantarki ce silar tashin gobarar

- Gwamnan jihar Katsina da mataimakinsa da mai bawa gwamna shawara a kan makarantun gaba da sakandire sun ziyarci jami'ar domin ganin irin barnar da gobarar tayi

Wata gobara mai ban mamaki ta babbake wasu sassa da ofisoshi a jami'ar Umaru Musa Yar'adua. Daga cikin gine-ginen da wutar ta kone akwai tsangayar karatun koyar wa, ofishin shugaban tsangayar karatun kimiyyar adana bayanai, ofishin jarrabawa da wasu ofisoshin malamai.

Duk da ba a san abinda ya haddasa gobarar ba, wasu da gobarar ta tashi a kan idonsu sun bayyana cewar wutar lantarki ce silar tashin gobarar.

Katsina:Gobara ta tafka barna a jami'ar UMYU

Gwamnan jihar Katsina; Aminu Bello Masari
Source: Depositphotos

Da suka ziyarci jami'ar domin gane wa idonsu, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, da mataimakinsa, Alhaji Mannir Yakubu, da mai bawa gwamna shawara a kan ilimin gaba da sakandire, Alhaji Bashir Ruwan Godiya, sun bukaci jami'ar ta kafa kwamitin da zai binciko dalilin afkuwar gobarar tare da yin alkawarin biyan ta'adin da gobarar ta yi.

DUBA WANNAN: Allah kyauta: An kashe mutane 20 a sabon harin 'yan bindiga a Kajuru

Kazalika, gwamna Masari ya bukaci 'yan asalin jrhar Katsina da ke zaune a Legas da su nema wa 'ya'yansu gurbin karatu a manyan makarantun jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel