An yanke wa wani mutum hukuncin daurin rai-da-rai kan laifin lalata yar dan’uwansa mai shekara 7

An yanke wa wani mutum hukuncin daurin rai-da-rai kan laifin lalata yar dan’uwansa mai shekara 7

Wata kotun Ikeja a ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu ta yanke wa wani mutum mai shekara 29, wanda ke aikin gyara tayoyin mota hukuncin daurin rai-da-rai, sakamakon yiwa yar dan’uwansa mai shekara bakwai fyade.

Justis Abiola Soladoye ta yanke hukunci akan mai laifin, Idowu Gbolahan na gida mai lamba 44, a unguwar Sanusi, Shomolu Lagos bayan ya amsa laifinsa a lokacin da aka gurfanar da shi bisa laifin yi wa yar karamar yarinya fyade.

Yayinda ake yanke ma Gbolahan hukuncin, mai shari’an ta bayyana cewa gwamnatin Jihar Legas na iya bakin kokarinta wajen ganin ta kau da masu aikata miyagun ayyuka, kuma wannan hukuncin zai zamo darasi ga sauransu.

An yanke wa wani mutum hukuncin daurin rai-da-rai kan laifin lalata yar dan’uwansa mai shekara 7

An yanke wa wani mutum hukuncin daurin rai-da-rai kan laifin lalata yar dan’uwansa mai shekara 7
Source: Twitter

Ta ce, “An gurfanar da mai laifin a kotu a yau kuma ya amsa laifinsa na fyade wanda ya saba ma sashi na 137 na dokar masu laifi a Legas na 2015."

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Najeriya ta daura laifin rikicin arewa kan sarakunan gargajiya

Kafin a yanke mishi hukuncin, Misis Fehinti Ogbemudia, jagoran yar sanda mai kara tace mai laifin yayi wa mai karan fyade, wacce ta ziyarci kakarta a ranar 11 ga watan Agusta 2018.

Sai mai laifin ya kama yarinyar ya kaita wani daki, inda ya danne ta, ihun nata ne ya ja hankalin makwabta inda suka kai mata dauki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel