Marasa kishi ne masu bukatar a tuge Buratai –Odeyemi

Marasa kishi ne masu bukatar a tuge Buratai –Odeyemi

Kwamared Oladimeji Odeyemi, masani kan bincike wanda ya shafi harkar ta’addanci wanda kuma shine mai wayar da kan farar hula akan harkokin ta’addaci na Najeriya, a wata tattaunawa yayi Magana dangane da zaben da akayi a kwanan baya da kuma wasu abubuwa makamantansa.

Ga yanda tattaunawar ta kasance:

Anyita maganar rundunar sojin Najeriya a labarai akan rawar da suka taka lokacin zaben 2019. Me zaka iya cewa akan rudunar sojin kafin zabe, lokaci da ake gudanar da zaben da kuma baya kamala shi?

Janar Tukur Buratai

Janar Tukur Buratai
Source: UGC

KU KARANTA:Jiragen ruwa 6 makare da man fetur da sauran kayayyakin amfani sun iso tashar jirgin ruwan Lagas

Yace: "Rawar da rundunar soji ta taka, musamman sojin kasa kafin zabe da kuma bayansa abu ne wanda yazo a lokaci da ake bukatarsa saboda sun taimaka wajen tsare ingancin zaben.

Sun kasance masu bada kwarin gwiwa gas aura jam’ian tsaro kamar yan sanda da sauransu. So da yawa suke ake nemowa lokaci kwantar da tarzoma.

Basu nuna bangarancin jam’iya ba yayin gudunar da aikinsu, kamar yadda aka samu musayar wuta tsakanin jami’an sojin da yan bangar siyasa a Jihar Rivers. Rudunar sojin tayi aiki cikin tsanaki da kuma kwarewa don haka sun cancanci a yaba musu matuka saboda wannan namijin kokari nasu."

Kana tunanin rudunar sojin bata kasance tana tare da wata jam’iyar siyasa ba yayin gudunar da aikinta?

"Hakikanin gaskiya, idan ka dubi tarihin Jami’an tsaron Najeriya da kuma dangantakarsu da wannan jagoranci na musamman sojin kasa wanda shine kashin bayan sojin, zaka yarda dani cewa rundunar tayi iya kokarinta wuri kaucewa nuna bangarancin jam’iya ya gudanar da ayyukanta.

Wannan tabbas abin yabawa ne domin yana nuna cewa lallai akwai ingantaccen jagoranci a fannin tsaro na sojin Najeriya. Rudunar sojin kasa ta Najeriya karkashin jagorancin Janar Tukur Buratai ba kawai kwarewa ta wajen gudanar da aiki ne abinda ya karu kana hadda dada wayar da kai akan rashin nuna bambanci jam’iya yan kadan daga cikin jama’ar da siyasar jam’iya bata gabansu.

Wannan jagoranci rudunar sojin Najeriya shine mafi kyawun da rundunar ta samu a daidai wannan lokacin. Tambaya akan ko rudunar na goyon baya wata jam’iyar siyasa bai taso ba yayin gabatar da aikinsu ba kafin zaben, lokaci zaben da kuma bayan zaben 2019.

Sun baiwa tsarin kulawar da ta dace don ganin cewa a gudanar da zabe mai tsafta. Matsaloli da kuma barazana da suka gaza faruwa hakan ya kasance ne saboda jajircewar sojin kasar wasu jihohi."

Akwai rahoto akan Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas. Baka tunanin wannan shima kan iya kasancewa cikas ne ga rudunar ta soji?

"Zan iya cewa rudunar sojin kasa karkashin jagorancin Janar Tukur Buratai ta nuna kwarewa da kuma hanyoyin na dubara wajen kawo karshe ta’addaci a yankin na Arewa maso Gabas."

A naka hasashen a matsayinka na kwararen akan harkar tsaro, wane mataki rudunar ta soji karkashin Buratai ta cinma wajen yaki da ta’addaci a yankin Arewa maso Gabas?

"So da yawa an sha fadi ba ma jami’ian tsaro kadai ba harma da wasu masana akan sha’anin daya shafi tsaro da jama’ar gari cewa cin yaki day a hada da ta’addanci ba abu ne mai sauki ba. Yaki da ta’addaci ba kamar wasan kwallon kafa bane wanda akeyi cikin dakika casa’in (90).

Hakikanin abinda ke faruwa a Arewa ta gabas shine tun zuwan wannan gwamnati an samu sauki hare-haren Boko Haram, duba ga cewa a gwamnati da ta gabata Boko Haram ta fara kafa tata Nahiyar ta daban da yunkuri fitar da na tsarin gwamnati daban da na kasa.

Wannan babban cigaba ne da aka samu wajen yaki da Boko Haram wanda ta kasance ta gudanar da hare-harenta a Abuja da kuma kananan hukumomi 14 a jihohi bakwai dake yankin Arewa ta gabas. A halin yanzu kuwa kananan hare-haren kawai suke iya kawai wanda ma yawancinsu na kunar bakin wake ne. A halin yanzu Boko haram bata da wannan halin na gudanar da hare-hare kamar yadda take a baya saboda tsauraran matakan da rudunar sojin ta dauka.

A cikin shekara hudu da suka wuce rundunar karkashin jagorancin Janar Buratai sun fitar da tsare-tsaren kawo karshen rikicin manoma da makiyaya.

Abu na uku shine kashe-kashen da suka hada da al’amuran siyasa wanda yafi yawa a Arewa ta tsakiya. A wannan wajen ne Laftanal Janar Buratai ya cancanci yabo ganin yadda yayi kokarin kawo wannan rikicin karshe duk kuwa rikici ne day a shafi kabilanci. Hanyoyin da rudunar tayi amfani dasu sun hada da tattaunawa, samar da abeben more rayuwa, cigaban al’umma, karfafa matasa da dai sauransu. Kamar yanda ka sani rudunar sojin ta gudanar da ‘Operation Last Hold’ a tsakanin farfajiyar yaki hakan kuwa nufin anzo karshe akan yaki da ta’addanci. Rudunar zata cigabda da wannan tsarin nata har sai tag a bayan yan ta’adda da kuma ta’addanci wannan yankin."

Akwai da’awa daga wurare da dama cewa Shugaba Buhari yayi waje da Buratai, kana ganin hakan abu ne daya dace kuwa?

"Wannan sam bai kamata ba, fadin hakan ma rashin kishin kasa ne daga wasu bara gurbin dake cikinmu da kuma yan kasashen waje dake goyon banyansu. Yin hakan zai maida kasar na baya ne domin tabbas zata ras abinda ta riga da ta samu bisa ga jajircewar rudunar sojin kasar nan a yankin Arewa maso gabas.

Yan ta’addar sun kasance suna da tutoci a kananan hukumomi aha hudu kafin zuwan Janar Buratai. Yanzu kuwa basu da ko daya don haka bas u iya ikirarin ko daya a fadin kasarmu.

Shugaban kasarmu kwararren soja ne hakan nema yasa yayi amfani da ilimi da kuma kwarewarsa wajen zaben Janar Buratai mutum da yafi dacewa day a kasance hafsin hafsoshin na sojojin Najeriya. Lura da yanayi kasar a yau tsige Buratai ba maganar dubawa bace."

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel