Nemo man fetur a Arewa ba zai ceto tattalin arzikin Najeriya ba - Sanata Murray-Bruce

Nemo man fetur a Arewa ba zai ceto tattalin arzikin Najeriya ba - Sanata Murray-Bruce

- Sanata Ben Murray-Bruce ya gargadi gwamnatin tarayya a kan dogewarta bisa neman man fetur a Arewa

- Dan majalisar ya ce man fetur bai shine zai ceto tattalin arzikin Najeriya ba

- Murray-Bruce ya bukaci gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wurin bayar da ilimi ga yara miliyan 12 da ke gararamba a kasar

Sanata mai wakiltan Bayelsa Ta Gabas a majalisar dattawa, Ben Murray-Bruce ya koka a kan yadda gwamnatin tarayya ta fi bayar da fifiko a kan nemo man fetur a Arewa a maimakon ilimantar da yara miliyan 12 da ba su zuwa makaranta a kasar.

Channels TV ta ruwaito cewa dan majalisar ya ce lamarin abin takaici ne duba da yadda Najeriya ta mayar da hankali a kan man fetur a lokacin da duniya ke kokarin gujuewa man fetur din.

DUBA WANNAN: 2019: Jiga-jigan PDP da yawa sun ci amanan jam'iyyar a Gombe - Dankwambo

Ku dena neman fetur a Arewa, ba zai ceto tattalin arzikin Najeriya ba - Sanata Ben Muray-Bruce

Ku dena neman fetur a Arewa, ba zai ceto tattalin arzikin Najeriya ba - Sanata Ben Muray-Bruce
Source: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa Sanata Murray-Bruce ya ce man fetur ba zai ceto Najeriya daga halin da ta ke ciki ba inda ya yi misali da kasar Venuzuela da ke da dimbin man fetur amma tattalin arzikin su bai habbaka ba.

Ya ce: "Mun fi kashe kudi wurin nemo man fetur a Arewa fiye da kokarin bayar da ilimi ga yara miliyan 12 da ba su zuwa makaranta a lokacin da duniya ke kokarin dena yayin man fetur. Venezuela kasar da tafi kowacce kasa a duniya yawan man fetur tana cikin talauci. Fetur ba zai warware matsalolin Najeriya ba."

Ya kara da cewa yawan al'ummar da ke Najeriya yana karuwa fiye da tattalin arzikin kasar kuma idan ba a dauki matakan da suka dace ba, al'amurra za su kara tabarbarewa a kasar.

"Yawan al'ummar mu yafi karfin tattalin arzikin mu. Yanzu duniya ta fara shirin komawa amfani da motocci masu aiki da lantarki ne hakan na nufin abubuwa za su tabarbare idan ba mu dauki mataki a yanzu ba. Shin mun shirya rayuwa ba tare da man fetur ba? Dole ya faru ko muna so ko bamu so.

A baya, Legit.ng ta ruwaito muku cewa shugaban hukumar man fetur na kasa NNPC, Maikanti Baru ya ce za a cigaba da neman man fetur a Arewa har sai an cimma nasara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel