Rundunar 'yan sanda ta kori manyan jami'an ta 9 saboda saba dokar aiki

Rundunar 'yan sanda ta kori manyan jami'an ta 9 saboda saba dokar aiki

Hukumar Kula da Rundunar 'yan sandan Najeriya, PSC ta amince da korar wasu manyan jami'an 'ya sanda guda tara daga aiki nan take saboda samunsu da saba dokokin aiki.

Hukumar ta kuma rage wa wasu jami'anta shida mukaminsu saboda samunsu da aikata wasu laifukan.

Kakakin PSC, Ikechukwu Ani ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne a wurin taron sauraron korafi karo na 5 da aka gudanar daga ranar 26 zuwa 27 na watan Maris a babban birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin tsohon sufetan 'yan sanda, Musuliu Smith.

Rundunar 'yan sanda ta kori manyan jami'an ta 9 saboda saba dokar aiki

Rundunar 'yan sanda ta kori manyan jami'an ta 9 saboda saba dokar aiki
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 2019: Jiga-jigan PDP da yawa sun ci amanan jam'iyyar a Gombe - Dankwambo

Sanarwar ta ce, "wadanda aka kora daga aiki sun hada da Abdul Ahmed mai mukamin sufritanda, SP Adamu Abare, DSP Osundu Christian, Samson Ahmidu da Pius Timiala. Sauran sun hada da mataimakan sufritanda hudu; Agatha Usman, Esther Yahaya, Idris Shehu da Usman Dass."

Hukumar ta PSG ta kuma bukaci mukadashin sufetan 'yan sanda ya sanar da ita hukuncin da aka yiwa 'yan sandan da aka ambaci sunayensu cikin rahoton cuwa-cuwar da aka samu wurin daukan sabbin 'yan sanda na 2011.

"An rage wa Oluwatoyin Adesope da Mansir Bako mukamansu daga SP zuwa DSP yayin da Gbenle Mathew; Tijani Saifullahi; Sadiq Idris da Alice Abbah aka rage musu mukami daga DSP zuwa ASP," inji Hukumar.

Ta kara da cewa an aike wa Sufeta Janar na 'yan sanda hukuncin da hukumar ta yanke a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun sakataren hukumar, Nnamdi Mbaeri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel