Gwamnatin Najeriya ta daura laifin rikicin arewa kan sarakunan gargajiya

Gwamnatin Najeriya ta daura laifin rikicin arewa kan sarakunan gargajiya

Ministan Tsaron Najeriya, Mansur Dan Ali ya bayyana cewa, sabbin bayanan sirri sun nuna cewa, akwai hannun wasu manyan sarakunan gargajiya a kashe-kashen da ake ci gaba da kaddamarwa a wasu yankuna na arewacin kasar.

Munanan hare-hare da ake daura alhakinsu akan yan bindiga na cigaba da aukuwa a yankin jihohin Arewa maso Yamma wadanda suka hada da jihohin Zamfara, Sokoto, da Katsina, tare da kisan fiye da mutum dari a yan watanni da suka gabata.

A yankin Arewa maso Gabas, yan kungiyan Boko Haram na cigaba da kai hare-hare wanda yawancin hare haren yafi shafar Borno, Yobe da Adamawa.

Kashe-kashe da yan bindiga ke yi a yankunan yasa rundunan soji da yan sanda kafa tashohi a wadannan jihohin, tare da alkawarin da shugaban Muhammadu Buhari ya dauka wajen inganta lamarin tsaro.

Gwamnatin Najeriya ta daura laifin rikicin arewa kan sarakunan gargajiya

Gwamnatin Najeriya ta daura laifin rikicin arewa kan sarakunan gargajiya
Source: UGC

A wata sanarwa da ya aika wa Jaridar Premium Times, a ranar Talata, 9 ga watan Maris, Ministan ya ce, sun gano cewa, sarakunan gargajiyar da ba a bayyana sunansu ba, na da hannu a hare-haren 'yan bindigar, amma ya lashi takocin cewa, za su fuskanci hukunci.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sojoji sun bar garin Borno kan barazanar tsaro

Ministan ya bukaci al’ummar jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da sauran sassan arewacin Najeriya da su tashi tsaye wajen bayar da goyon baya ga yunkurin gwamnati na magance tashin hankalin, lura da cewa, sojojin da ke filin-daga ba za su iya yakar maharan su kadai ba.

Ministan ya kara da cewa tsayar da ayyukan hake-hake da aka yi a fadin kasar ya kasance daga cikin shawarwarin da gwamnatin ta daukaka don tabbatar da kwanciyar hankali a yankin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel