Yanzu Yanzu: Sojoji sun bar garin Borno kan barazanar tsaro

Yanzu Yanzu: Sojoji sun bar garin Borno kan barazanar tsaro

Rahotanni sun kawo cewa an janye rundunar sojojin Najeriya daga garin Jakana a karamar hukumar Konduga da ke jihar Borno.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kwashe al’umman garin zuwa Maiduguri, babbar birnin jihar Borno.

Rundunar sojin tace an dauki matakin ne saboda dalilai na tsaro.

Yanzu Yanzu: Sojoji sun bar garin Borno kan barazanar tsaro

Yanzu Yanzu: Sojoji sun bar garin Borno kan barazanar tsaro
Source: Depositphotos

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, undunar sojin sama (ATF) ta Ofireshon Lafiya Dole ta lalata wata mafakar 'yan ta'addar kungiyar 'Islamic State of West Africa Province (ISWAP) tare da kashe mayakan kungiyar da dama a garin Tumbun Zarami da ke gabashin jihar Borno.

ATF ta samu wannan gagarumar nasara ne a ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu, a cigaba da atisayen 'ofireshon YANCIN TAFKI', da aka kirkira domin kakkabe burbushin kungiyar ISWAP daga kasashen gefen tekun Chadi.

Rundunar sojin sama, yayin gudanar da wani atisaye a sararin samaniya, ta gano wata mafaka da mayakan ISWAP masu yawa ke fake wa ta hanyar amfani da na'urori na musamman a jirginsu na yaki.

KU KARANTA KUMA: Atiku na kamun kafa da Amurka don ta tabbatar dashi a matsayin shuagaban kasar Najeriya

Bayan gano sansanin ne sai rundunar ta aika wasu jiragenta biyu na musamman (Alpha Jets) da suka yi kasa-kasa da sansanin ta hanyar yi masu ruwan bama-bamai da luguden wuta. Lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mayakan kungiyar da dama, kamar yadda Ibikunle Daramola, darektan yada labarai da hulda da jama'a na rundunar soji sama ya sanar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel