Zan sadaukar da kaina wurin koyawa matasa siyasa - Tsohon shugaban majalisar dattawa

Zan sadaukar da kaina wurin koyawa matasa siyasa - Tsohon shugaban majalisar dattawa

- Tsohon shugaban majalisar dattawa ya yi alkawarin zage dantse don ya koyawa matasa siyasa

- Ya yi bayanin hakan jiya a Abuja a lokacin da ake gabatarda taron bikin murnar cikarshi shekaru 71 a duniya

A jiya ne tsohon shugaban majalisar dattawa na kasa, Sanata David Mark, ya bukaci manyan 'yan siyasar kasar nan da su koyawa matasa masu tasowa siyasa, domin su ne wadanda zasu mulki kasar a nan gaba.

Da yake jawabi jiya a wurin taron bikin murnar cikarshi shekaru 71 a duniya, Sanatan ya bayyanawa 'yan uwanshi 'yan siyasa da abokan arziki cewa: "Daga yau zan sadaukar da lokacina da karfina wurin koyawa matasan mu na yanzu siyasa. Saboda muna son shugabanni na gari, wadanda za su kawowa kasarmu cigaba."

Zan sadaukar da kaina wurin koyawa matasa siyasa - Tsohon shugaban majalisar dattawa

Zan sadaukar da kaina wurin koyawa matasa siyasa - Tsohon shugaban majalisar dattawa
Source: UGC

A wata sanarwa da mataimakin shi a fannin sadarwa ya fitar, Paul Mumeh, tsohon shugaban majalisar dattawan ya bukaci 'yan siyasar Najeriya da su bi sahun shi domin koyawa yara siyasa, ya ce ya samu kwarewa sosai a harkar siyasa a wannan 'yan shekarun, saboda haka zai yi amfani da kwarewar shi wurin koyawa 'yan baya abinda basu sani ba.

KU KARANTA: Jerin Ministocin da shugaba Buhari zai koma mulki da su

Sanatan kuma ya bada shawara akan manyan hukumomi da suke mu'amala da 'yan siyasa da su zama na gari, musamman irin su: Hukumar zabe ta kasa, jam'iyyun siyasa, hukumomin tsaro, da kuma kafannin sadarwa, akan su bi yadda doka ta tsara wurin gabatar da ayyukan su.

A karshe babban Faston cocin St Mulumba Catholic Chaplaincy, Rev. Father Innocent Jooji, ya yabawa Sanatan da irin halaye kyawawa da yake da su na siyasa, da kuma irin kokarin da ya yi lokacin da yana shugaban majalisar dattawa, wanda ya yi shekaru takwas a kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel