Buratai ya yi alkawarin inganta rayuwar sojojin Najeriya

Buratai ya yi alkawarin inganta rayuwar sojojin Najeriya

- Shugaban hukumar soji ta kasa, Tukur Yusuf Buratai ya ce babban burinsa shine ya ga ya inganta rayuwar jami'an sojin Najeriya

- A jiya ne dai shugaban hukumar sojin ya kaddamar da wasu sabbin gidaje da hukumar ta gina a jihar Bauchi don samarwa da jami'an ingantaccen wurin bacci

Shugaban hukumar sojojin Najeriya, Tukur Yusuf Buratai, ya ce babban burinsa shine yaga ya inganta jin dadi da kuma lafiyar jami'an sojojin Najeriya

Babban hafsan sojin ya bayyana hakan jiya Litinin a jihar Bauchi, a lokacin da ya ke gabatar da sabbin gidajen kwana da aka ginawa sojojin a jihar ta Bauchi.

Buratai ya ce a yanzu haka akwai ayyukan da ake gudanarwa a fadin kasar nan, wadanda iya jami'an hukamar soji ne kawai za su amfana da su.

Buratai ya yi alkawarin inganta rayuwar sojojin Najeriya

Buratai ya yi alkawarin inganta rayuwar sojojin Najeriya
Source: UGC

Shugaban hukumar sojin ya bayyana cewa, an kashe kudi da yawa wurin samarwa da jami'an tsaftacaccen wuraren kwana, duk kuwa da matsalar rashin isashen kudi da ake fama dashi a hukumar, sannan ya bukaci jami'an da su lura sosai wurin kula da gidajen.

KU KARANTA: Muhimman abubuwan da ba ku sani ba dangane da CP Wakili

Bayan haka Buratai, ya yi kira ga jami'an sojoji da su ba wa sauran jami'an tsaron kasar nan hadin kai wurin gabatar da ayyuka da za so kawo cigaban kasa.

A lokacin da yake na shi jawabin Manjo Janar James Olubumi Akomoleke, ya bayyana cewa gidajen da shugaban hukumar sojin ya gabatar suna daga cikin kokarin da shugaban hukumarr sojin ya ke yi na ganin ya inganta rayuwar jami'an hukumar soji na kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel