Atiku na kamun kafa da Amurka don ta tabbatar dashi a matsayin shugaban kasar Najeriya

Atiku na kamun kafa da Amurka don ta tabbatar dashi a matsayin shugaban kasar Najeriya

Rahotanni sun kawo cewa dan takarar Shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) wanda ya sha kaye, Alhaji Atiku Abubakar, na kama kafa da kasar Amurka domin ta tabbatar dashi a matsayin sahihin zababben Shugaban kasar Najeriya.

Wani hadimin dan takarar Shugaban kasar, Paul Ibe, wanda Legit.ng ta tuntuba don jin martani, yayi alkawarin sake kira. Amma bai aikata hakan ba a daidai wannan lokacin.

Atiku, wanda ya fadi zaben Shugaban kasa bayan ya sha kaye a hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), na kamun kafa da Amurka ta hannun lauyoyi biyu a Washington DC, Centre for Responsive Politics (CRP) ta ruwaito.

Atiku na kamun kafa da Amurka don ta tabbatar dashi a matsayin shugaban kasar Najeriya

Atiku na kamun kafa da Amurka don ta tabbatar dashi a matsayin shugaban kasar Najeriya
Source: Facebook

Kungiyar bincike da aka kafa don bibiyar kudi a siyasar Amurka da kuma tasirinsa kan zabuka da munufofin jama'a, a ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu tace: "Da taimakon wasu manyan lauyoyi a Washington DC, wani dan takarar shugaban kasar Najeriya na neman taimako a kalubalantar sakamakon zaben da yake yi bayan ya sha kaye."

Rahoton yayi ikirarn cewa Atiku ya hade da wadanda ke kewaye da Trump, “bayan ya yo hayan masana harkar siyasa irinsu Riva Levinson, wanda yayi aiki tare da Paul Manafort, da Brian Ballard, manyan na hannun daman Trump. Kamar dai sauran shugabannin dumiya da ke neman kafa gwamnatinsu a wajen Trump, Abubakar ya tsaya a otel din Trump a Washington D.C."

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sojoji sun bar garin Borno kan barazanar tsaro

Rahoton ya ci gaba da ikirarin cewa dan takarar Shugaban kasar na PDP, ta hanyar hakan, yana shiga cikin yan siyasa kamar Shugaban adawar Venezuelan Juan Guaidó wajen kamun kafa da Amurka.

Don cimma hakan, rahoton yace Atiku ya biya $30,000 na kwangilan kwanaki 90, a cewar wani rahoton FARA, a ranar 24 ga watan Maris, ya nuna cewa tsohon jami’in sashin shari’a Bruce Fein da kamfaninsa Fein & DelValle PLLC sun yi rijist a matsayin jami’an kasar waje a madadin Atiku.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel