Sanata Ndume ya bayyana dalilin da yasa ya ziyarci Osinbajo

Sanata Ndume ya bayyana dalilin da yasa ya ziyarci Osinbajo

A jiya Litinin 8 ga watan Afrilu ne mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi ganawar sirri da tsohon jagoran majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Duk da cewa ba a bayyana abinda suka tattauna ba, Sanatan ya karyata jita-jitan da wasu keyi na cewa ya ziyarci fadar shugaban kasar ne saboda takarar da ya ke yi na kujerar shugabancin majalisar dattawa.

Ndume ya bayyana niyarsa na yin takarar kujerar shugabancin majalisar dattawa duk da cewa shugabanin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun goyi bayan Sanata Ahmed Lawan domin zama shugaban majalisar.

DUBA WANNAN: 2019: Jiga-jigan PDP da yawa sun ci amanan jam'iyyar a Gombe - Dankwambo

Ndume ya bayyana dalilin da yasa ya ziyarci Osinbajo

Ndume ya bayyana dalilin da yasa ya ziyarci Osinbajo
Source: UGC

Bayan ganawarsa da mataimakin shugaban kasar, Sanatan ya ki yin magana da manema labarai na gidan gwamnati.

A lokacin da aka masa tambaya a kan cewa ko sai janye daga takarar shugabancin majalisar, ya ki bayar da amsa mai gamsarwa.

Sai dai ya ce har yanzu ana tattaunawa a kan lamarin.

"Ba zan iya tsokaci a kan lamarin ba saboda ina shawarwari da wasu," inji shi.

A hirar da ya yi da The Nation, Ndume ya yi bayanin cewa ya ziyarci fadar shugaban kasar ne saboda tattaunawa a kan tallafi da za a kaiwa al'ummar Borno.

"Ba batun siyasa ta bane ta sa na gana da mataimakin shugaban kasa. Ba muyi wata maganar siyasa ba," inji Ndume.

"Mataimakin shugaban kasa ya damu matuka a kan halin da al'ummar Borno ke ciki na rashin tsaro. Dama na saba tuntubar sa saboda ayyukan bayar da tallafi ga al'ummar jihar mu. Wannan shine abinda muka tattauna da shi.

"Banyi masa magana a kan takarar da na keyi na neman zama shugaban majalisa ba kuma shima bai min maganan ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel