Rikicin Zamfara: Gwamnati na samun bayanan sirri – Fadar shugaban kasa

Rikicin Zamfara: Gwamnati na samun bayanan sirri – Fadar shugaban kasa

Kakakin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mallam Garba Shehu ya bayyana dalilan da ya sa gwamnatin tarayya ta dakatar da hakar ma’adinai a jihar Zamfara.

Mallam Garba yace gwamnatin tarayya ta samu wasu bayanai na sirri kan nasabar da ke tsakanin munanan hare-haren yan bindiga da ake kai wa al’umman yankin da kuma hakar ma’adina da ke gudana a yankin.

Sai dai kakakin Shugaban kasar bai fito fili ya bayyana irin bayanan da gwamnatin ta samu ba akan nasabar da ke tsakanin hakar ma’adinan da ta’assar da ke afkuwa a jihar ta Zamfara.

Amma ya bayyana cewa matakin da aka dauka na da alaka da matsaloliin da jihar ke fuskanta.

Rikicin Zamfara: Gwamnati na samun bayanan sirri – Fadar shugaban kasa

Rikicin Zamfara: Gwamnati na samun bayanan sirri – Fadar shugaban kasa
Source: Twitter

Ya ce baya ga 'yan Najeriya, akwai wadanda ba 'yan kasa ba da dama da suke aikin hakar ma'adinai inda wasu ke yi bisa ka'ida wasu kuma suna yi ba bisa ka’ida ba.

Garba ya bayyana cewa ya kamata jama'a su yi hakuri domin gwamnati na nan na bincike kuma jama'a za su samu gamsuwa da sakamakon da gwamnati za ta fitar.

KU KARANTA KUMA: Niger ta gabas: Sai na kwato hakkina – Sani Musa

Ya ce akwai hadakar rundunonin da aka kafa na sojojin kasa da na sama da sauran jami'an tsaro inda ya bayyana cewa an ba su umarnin yin maganin duk irin fitinar da ta kunno kai a fadin kasar.

Haka kuma, ya bayyana cewa gwamnatin kasar na takaicin kara kunno kan irin wannan matsala ta rashin tsaro.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel