Bankin musulunci ya bawa gwamnatin Najeriya dala miliyan 532

Bankin musulunci ya bawa gwamnatin Najeriya dala miliyan 532

Bankin Musulunci na duniya ya ba wa gwamnatin Najeriya tallafin kudi kimanin naira biliyan 200, domin bunkasa masana'antu da kuma gyara a hukumar aikin Hajji ta kasa

Ministar kudi, Zainab Ahmed Shamsuna, ta karbawa gwamnatin tarayya kudi kimanin dala miliyan 532, wanda ya yi dai-dai da naira biliyan 191 a kudin Najeriya, daga wurin Bankin Musulunci.

Ministar ta karbi kudin a jiya Litnin 8 ga watan Afrilu, a Marrakesh, dake kasar Morocco, kudin wanda aka bayyana shi a matsayin taimako ga gwamnatin tarayya daga Bankin Musulunci.

Bankin musulunci ya bawa gwamnatin Najeriya dala miliyan 532

Bankin musulunci ya bawa gwamnatin Najeriya dala miliyan 532
Source: Twitter

Ministar ta ce, sun yi yarjejeniyar da bankin wurin karbar kudin akan za ayi gyar-gyare a kwamitin aikin hajji ta kasa, da kuma bunkasa harkar noman auduga, da gyara masana'antu na saka.

A sanarwar da wani mai bawa ministar shawara na musamman a fannin sadarwa, Paul Ella Abechi, ya ce, "an bawa kwamitin Hajji da Umrah ta Najeriya dala miliyan 243 kimanin naira biliyan 88 a kudin Najeriya, sannan an bawa ma'aikatar bunkasa kasuwanci ta Najeriya dala miliyan 280, wanda ya yi dai dai da naira biliyan 100 a kudin Najeriya."

KU KARANTA: Muhimman abubuwan da ba ku sani ba dangane da CP Wakili

Banki ya ba wa kwamitin aikin Hajji ta kasa dala miliyan 243 domin gyare-gayre ga hukumar, sannan kuma ya ba wa ma'aikatar bunkasa kasuwanci ta kasa dala miliyan 280 domin, bunkasa harkar noman auduga, da kuma gabatar da gyare-gyare ga masana'antu na saka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel