Gwamnatin tarayya ta yi umurnin karin jiragen kasa 2 don sufuri a Abuja-Kaduna

Gwamnatin tarayya ta yi umurnin karin jiragen kasa 2 don sufuri a Abuja-Kaduna

Gwamnatin Tarayya ta bada umurnin karin jiragen kasa biyu da zai dunga zarya a hanyar jirgin kasan Abuja-Kaduna don rage matsalar yawan fasinjoji.

Mista Rotimi Amaechi, Ministan Sufuri, ya bada umurnin a ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu a lokacin da yake ziyarar gani da ido na wata-wata na ayyukan hanyar jirgin Lagoas-Ibadan a Oogueru, Ibadan.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa akwai matsalar yawan fasinjoji a tashar jirgin kasa na Abuja-Kaduna saboda ayyukan masu garkuwa da mutane da ke gudana a hanyar Abuja-Kaduna.

Ameachi yace hukumar kula da tashoshin jiragen kasa na Najerya zasu kai karin jiragen kasa biyu daga Itakpe-Warri zuwa hanyar.

Gwamnatin tarayya ta yi umurnin karin jiragen kasa 2 don sufuri a Abuja-Kaduna

Gwamnatin tarayya ta yi umurnin karin jiragen kasa 2 don sufuri a Abuja-Kaduna
Source: UGC

Yayi gargadin cewa za a hukunta duk wani jami’i da aka kama yana siyar da tikiti ba bisa doka ba.

KU KARANTA KUMA: A kai kujerar mataimakin Shugaban majalisar dattawa kudu maso gabas – Kalu ya roki APC

“Zamu kama duk wanda muka sama yana siyar da tikiti, dogon layin fasinjoji da ake fuskanta ba komai bane illa karamcin ji

ragen kasa da aka samu.

“Mun siya wadannan jiragen ne saboda mutane su samu wajen zama. Amman mutane suna tsaye, bai kamata su kasance a tsaye ba. Amman na bada umurni cewa a kai jiragen kasa gida biyu daga Itakpe-Warri zuwa Kaduna-Abuja. Wannan ce rana na farko da zan bada wannan umurnin."

Ameachi ya bayyana cewa zai yi wuya ace an gudanar da aikin kula da fasinjoji dake tsaye a cikin jirgin saboda yawan su.

Ameachi, ya bayyana cewa har sai idan an samu alaka tsakanin Itakpe-Ajaokuta-Warri zuwa Lokoja da Abuja a lokacin da za a samu karin fasinjoji da zasu yi amfani da jirgin kasa a wannan yankin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel