Wadanda ake neman kakabawa shugabancin Majalisa ba za su kai labari ba – Dogara

Wadanda ake neman kakabawa shugabancin Majalisa ba za su kai labari ba – Dogara

Kakakin majalisar wakilai na tarayya, Honarabul Yakubu Dogara, yayi magana a game da shugabancin majalisar kasar inda yace ya kamata ne a bari ‘yan majalisa tarayya su zabi duk wanda su ke so.

Kamar yadda mu ka ji, Rt. Hon. Yakubu Dogara yayi wannan bayani ne jiya Litinin 8 ga Watan Afrilun 2019 a wajen taron wayarwa sababbin Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai kai da aka shirya a cikin a babban birnin tarayya Abuja.

Yakubu Dogara yake nuna cewa, kokarin da wasu ke yi na kakabawa majalisa wanda za su shugabance ta a bana, ba zai kai ga ci ba. Yanzu ya zama dole shugaban majalisar wakilan ya bar kujerar sa a bana bayan ya sauya-sheka zuwa PDP.

KU KARANTA: A bi Liman ko kuma a canza Masallaci – Sanatan Katsina ya fadawa Ndume

Dogara yake cewa a tarihi, irin wannan shiri na zakulo shugabannin majalisa daga waje bai taba aiki a Najeriya ba. Kakakin majalisar na Najeriya yake cewa wadanda ke neman mukamai da kan su, za su fi dacewa da su rike majalisar tarayya.

Wannan ya sa shugaban majalisar mai neman barin gado ya samu damar bada shawara ga sababbin shiga majalisar ta tarayya da su tsaya su zabi wakilai na gari wadanda su ka dace da jan ragamar su na tsawon shekara 4 masu zuwa a gaba.

KU KARANTA: Sanata APC ya nunawa Jam'iyya kunnen-kashi a Majalisa

A jawabin sa, yace cewa akwai bukatar a samu shugabannin da za su taka irin rawar da su ka taka a majalisa ta 8, ko kuma ma a samu wadanda za su yi abin da ya zarce na su. Dogara ya kuma nemi ayi wa sashe na 143 na dokar kasa garambawul.

Rt. Hon. Dogara yake cewa akwai bukatar ‘yan majalisar tarayya su yi wa wannan sashe na kundin tsarin mulkin Najeriya kwaskwarima, domin kuwa idan ba hakan aka yi ba, ba zai taba yiwuwa a iya tsige shugaban kasar Najeriya a majalisa ba.

Jam’iyyar APC dai tace dole ‘Ya ‘yan ta sun marawa Sanata Ahmad Lawan da kuma Honarabul Femi Gbajabiamilla a majalisar dattawa da ta majalisar wakilai wanda wannan bai yi wa wasu dadi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Online view pixel