Niger ta gabas: Sai na kwato hakkina – Sani Musa

Niger ta gabas: Sai na kwato hakkina – Sani Musa

- Alhaj Mohammed Sani Musa yace zai bi hakkinsa a kotun koli

- Musa ya bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu yayinda yake fafutukar ganin karshen abun

- Zababben sanatan na APC yace yana da tabbacin samun nasara a kotun koli ta hayar dage umurnin kotun daukaka kara

Zababben sanata na yankin Niger ta gabas a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Mohammed Sani-Musa, ya bayyana cewa zai kwato yancinsa a kotun koli.

Mista Sani Musa ya bayyana haka ne a wani jawabi da yayi a ranar Talata, 9 ga watan Afrilu a bayyana ra’ayinsa da yayi ga hukuncin kotun daukaka kara.

Zababben sanatan, wanda hukumar zabe na kasa mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa ya lashe zabe, kasancewa ya samu mafi yawan kuri’u, ya bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu yayinda yake kokarin ganin abun da za ture ma buzu nadi a kotun koli.

Niger ta gabas: Sai na kwato hakkina – Sani Musa

Niger ta gabas: Sai na kwato hakkina – Sani Musa
Source: Facebook

Yayin da yake bayyana rashin amincewarsa akan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, yace zai cigaba da bin duddugen lamarin har zuwa iya lokacin da kotun koli zata yanke hukunci mai ma’ana.

Haka zalika, ya tabbatar wa magoya bayanshi cewa su kwantar da hankulan su, ya kuma kara da cewa ya lashe zaben fidda gwanin na jam’iyyar APC wanda aka gudanar a mazabar sa.

KU KARANTA KUMA: A kai kujerar mataimakin Shugaban majalisar dattawa kudu maso gabas – Kalu ya roki APC

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke zaben Mohammed Sani wanda aka kaddamar a matsayin wanda ya lashe zaben sanata a yankn Niger ta gabas a karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Justis Adah ya yanke hukuncin ne bayan soke umurnin wata babbar kotun tarayya da ke Abuja akan hujjar cewa kotun bata da hurumin sauraron lamarin saboda doka ta hana hakan.

Alkalin ya umurci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta ba Sanata Umaru takardar shaidar cin zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel