A kai kujerar mataimakin Shugaban majalisar dattawa kudu maso gabas – Kalu ya roki APC

A kai kujerar mataimakin Shugaban majalisar dattawa kudu maso gabas – Kalu ya roki APC

Zababben sanatan Abia ta Arewa, Dr. Orji Uzor Kalu, a ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu ya roki shugabancin jam’iyyar All Progressive Congress (APC), da su kai kujerar mataimakin Shugaban majalisar dattawa zuwa yankin kudu maso gabas.

Kalu wanda ya yi wannan rokon a taron wayar da kan zababbun sanatoci da yan majalisar wakilai ya bayyana cewa, kai kujerar matamakin Shugaban majalisar dattawa yankin kudu ta gabas zai yi daidai da banbancin iri da ke kasar.

Yace banbancin iri da ke kasar, shine kyawun kasar.

Ya bayyana cewa ya kamata APC ta duba banbancin iri a matsayinta na jam’iyya, saboda “banbancin ne karfinmu.”

A kai kujerar mataimakin Shugaban majalisar dattawa kudu maso gabas – Kalu ya roki APC

A kai kujerar mataimakin Shugaban majalisar dattawa kudu maso gabas – Kalu ya roki APC
Source: Depositphotos

Yace: “Ni mai tsananin biyayya ne ga jam’iyya. Jam’iyyar ta rigada ta kasabta matsayin Shugaban majalisar dattawa. Ba zan taba kin yin biyayya ga jam’yyar ba. Jam’iyyar na da karfin iko.

“Abunda nake nema daga jam’iyyar shine ta kai kujerar taimakin Shugaban majalisar dattawa yankin kudu maso gabas, saboda kada na bijire ma jam’iyyar ta hanyar bin ta karkashin kasar majalisa, wanda ina da ikon yin hakan, idan aka barni nayi hakan.

KU KARANTA KUMA: Kotun daukaka kara ta soke zaben zababben sanatan APC Sani Musa

“Abunda nake nema yayinda jam’iyyar ta mika kujerar Shugaban majalisar dattawa ga arewa ta gabas, sai su mika na mataimakin Shugaban majalisar yankin kudu maso gabas. Saboda kada nayi takara ba bisa tsari ba.

“Zan iya takara da duk mutumin da ya fito daga yankin kudu maso gabas ko masu ruwa da tsaki na kudu maso gabas suje su yanke hukunci abunda yankin ke so a tsakannsu.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel