Kotun daukaka kara ta soke zaben zababben sanatan APC Sani Musa

Kotun daukaka kara ta soke zaben zababben sanatan APC Sani Musa

- Kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke zaben Mohammed Sani wanda aka kaddamar a matsayin wanda ya lashe zaben sanata a yankin Niger ta gabas

- Justis Stephen Adahya kaddamar da Sanata David Umaru a matsayin zababben sanatan Niger ta gabas

- Justis Adah ya yanke hukuncin ne bayan soke umurnin wata babbar kotun tarayya da ke Abuja

Kotun daukaka kara da ke Abuja, ta soke zaben Mohammed Sani wanda aka kaddamar a matsayin wanda ya lashe zaben sanata a yankin Niger ta gabas a karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Kotun daukaka karan a wani hukunci da Justis Stephen Adah ya zartar, ya kaddamar da Sanata David Umaru a matsayin zababben sanatan Niger ta gabas, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Justis Adah ya yanke hukuncin ne bayan soke umurnin wata babbar kotun tarayya da ke Abuja akan hujjar cewa kotun bata da hurumin sauraron lamarin saboda doka ta hana hakan.

Kotun daukaka kara ta soke zaben zababben sanatan APC Sani Musa

Kotun daukaka kara ta soke zaben zababben sanatan APC Sani Musa
Source: Depositphotos

Alkalin ya umurci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta ba Sanata Umaru takardar shaidar cin zabe.

KU KARANTA KUMA: Babu rabuwar kai tsakanin Alkalai, Inji kotun koli

Da yake martani ga hukuncin, Sanata Umaru yace hukuncin ya wanke shi. Ya yi godiya ga Allah da magoya bayansa wadanda suka tsaya mai.

Sai dai, tawagar lauyoyi da ke wakiltan Sani Musa sun nuna kudirin son daukaka kara zuwa kotun koli biyo bayan umurnin kotun daukaka karan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel