Ba hako fetur kurum ya sa Buhari ya damu da Neja-Delta ba – Osinbajo

Ba hako fetur kurum ya sa Buhari ya damu da Neja-Delta ba – Osinbajo

Mun ji cewa Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana shirin da gwamnatin tarayya da shugaba Muhammadu Buhari yake jagoranta ta ke da shi a yankin Neja-Delta.

Yemi Osinbajo ya bayyana cewa tanadin shugaba Buhari a yankin na Neja-Delta mai arzikin mai ya zarce maganar hako fetur. Mataimakin shugaban kasar yayi wannan bayani ne lokacin da yayi jawabi a jami’ar Maritime kwanan nan.

Mai ba mataimakin shugaban kasar shawara, Mista Edobor Iyamu, shi ne ya wakilici Mai gidansa wajen wannan biki na yaye ajin farko a babbar makarantar koyon harkar aikin ruwa da ke cikin Okerenkoko a Garin Warri ta jihar Delta.

Edobor Iyamu yake cewa gwamnatin Buhari tana da niyyar ganin an samu cigaba a yankin na Neja-Delta da ke kudu maso kudancin kasar. Daga cikin ayyukan da gwamnatin nan ta kawo domin inganta rayuwar yankin akwai sharar Ogoni.

KU KARANTA: Kamfanin fetur na Shell zai yi wasu ayyuka a Najeriya

Bayan nan, Hadimin mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa an kawo tsarin gina kananan matatun man fetur saboda ganin an rage barnar danyen fetur a Yankin. Edobor Iyamu yace za kuma a tada jami’ar ta Maritime tayi fice a ko ina.

Iyamu yace nan gaba kadan za a rika maganar irin Baiwar da Allah yayi wa jama’an yankin, bayan kuma albarkatun karkashin kasa da ake hakowa na fetur. Mai ba Osinbajo shawara yace wannan yana cikin manufofin gwamnatin shugaba Buhari.

Shugaban majalisar wannan jami’a watau Timipre Sylva, da Shugaban kungiyar NIMASA na kasa Dakuku Peterside, da kuma mukaddashin gwamnan jihar Delta duk sun yi jawabi a wajen wannan biki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel