Kokarin mu ne zai sa 'yan Najeriya su zabe mu a 2023 - Jam'iyyar APC ta bugi kirji

Kokarin mu ne zai sa 'yan Najeriya su zabe mu a 2023 - Jam'iyyar APC ta bugi kirji

Jam'iyyar APC ta ce za ta yi iya bakin kokarinta, wurin ganin ta gabatar da aiki a kasar nan, wanda zai bata daamar lashe zaben shekarar 2023

Mai magana da yawun jam'iyyar APC na kasa, Malam Lanre Issa-Onilu, ya bukaci 'yan Najeriya su yankewa jam'iyyar APC hukunci da kansu akan irin aiyukan da ta gabatar.

A wata hira da ya yi da 'yan jarida Abuja, Issa-Onilu ya ce, jam'iyyar APC za ta kara samun cigaba a shekarar 2023, ganin irin abubuwan da suka faru a wannan zaben da ya gabata, ciki kuwa hadda yadda jam'iyyar APC ta buga shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kasa, cikin sauki.

Kokarin mu ne zai sa 'yan Najeriya su zabe mu a 2023 - Jam'iyyar APC ta bugi kirji

Kokarin mu ne zai sa 'yan Najeriya su zabe mu a 2023 - Jam'iyyar APC ta bugi kirji
Source: Depositphotos

Ya ce mutane kansu ya waye yanzu, suna amfani da cancanta da kuma irin aikin da mutum ya yi musu, ba kamar halin da ake ciki a shekarun baya ba, da ake zaune cikin duhun kai.

"Yanzu mun gane cewa hanya daya ce zamu bi mu lashe zaben shekarar 2023, ta hanyar gabatarwa da 'yan Najeriya aiki, inda su da kansu zasu san cewa jam'iyyar APC ta yi aiki da kyau. Saboda haka muna da tabbacin yanayin aikin mu shine zai kai mu ga gaci a shekarar 2023," in ji shi.

KU KARANTA: Jerin Ministocin da shugaba Buhari zai koma mulki da su

A bangaren shari'ar alkalin alkalai na Najeriya, Walter Onnoghen, wanda a yanzu haka ya ajiye aikinsa, Issa-Onilu ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi amfani da dokar kasa ne ya yanke hukunci akan lamari.

Issa-Onilu ya ce, sakamakon zaben 2019, wanda jam'iyyar APC mai mulki ta fadi a jihar Bauchi, Adamawa, Sokoto da jihar Oyo, hakan yana nuni da cewar jam'iyyar APC ta bawa al'umma damar zuwa su zabi duk wanda suke so, sannan kuma suna da damar zuwa kotu don gabatar da kara idan suka ga abinda ba dai-dai ba, ba kamar irin mulkin mallakar da jam'iyyar PDP ta gabatar a baya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel