'Yan fashi sun kashe mutane bakwai a wani hari da suka kai banki a jihar Ondo

'Yan fashi sun kashe mutane bakwai a wani hari da suka kai banki a jihar Ondo

- Matsalar tsaro dai a Najeriya ta na kara samun koma baya, yayinda kowanne yanki a kasar nan suke fama da matsalar 'yan ta'adda, da suka hada da 'yan fashi, masu garkuwa da mutane, barayin shanu, 'yan boko haram da sauransu

- A jiya ne wasu 'yan fashi suka kai wani mummunan hari wani banki a jihar Ondo, inda suka kashe mutane bakwai a bankin

A jiya Litinin ne 8 ga watan Afrilu 2019, wasu 'yan fashi suka kai hari wani banki a Ido-ani, cikin karamar hukumar Ose da ke jihar Ondo, inda suka kashe mutane bakwai a kokarin da su ke na satar kudi a bankin.

Fashin wanda muka samu rahoton sun gabatar da shi da misalin karfe 2 na rana, a wani banki wanda yake a garin Isewa.

Majiyarmu LEGIT.NG ta samu rahoton cewa mutanen da abin ya shafa sun hada da, ma'aikatan bankin guda biyar, wani malamin makaranta wanda yaje bankin don cire kudi, da kuma wani jami'in dan sanda guda daya.

'Yan fashi sun kashe mutane bakwai, a wani hari da suka kai banki a jihar Ondo

'Yan fashi sun kashe mutane bakwai, a wani hari da suka kai banki a jihar Ondo
Source: UGC

'Yan fashin sun saci makudan kudade, wanda suka shafe wurin awa daya suna diba.

Wasu wanda aka yi fashin akan idon su sun bayyana cewa 'yan fashin sun shiga cikin bankin ne, inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi, bayan sun yi amfani da bam wurin fasa kofar bankin.

Sai dai kuma an ce anyi kokarin sanar da jami'an soji da kuma rundunar 'yan sanda da suke yankin don su kawo dauki, kafin su karaso wurin 'yan fashin sun gama fashin na su sun gudu.

KU KARANTA: Jerin Ministocin da shugaba Buhari zai koma mulki da su

Banda mutanen da suka rasa rayukan su, mutane da yawa sun samu raunika da dama, inda aka garzaya da su asibiti mafi kusa domin karbar magani.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, Femi Joseph, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya kuma bayyana cewa sun kama daya daga cikin 'yan fashin, wanda a yanzu haka ana gabatar da bincike akan shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel