Jirgin kasa ya murkushe mabaraci har lahira

Jirgin kasa ya murkushe mabaraci har lahira

Hukumar jiragen kasan Najeriya NRC ta tabbatar da cewa daya daga cikin jiragenta ya murkushe wani mai bara har lahira a unguwar Mushin dake jihar Legas ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu, 2019.

Manajan NRC na jihar Legas, Jerry Oche, ya tabbatar da hakan yayinda yake jawabi ga manema labarai a jihar.

Kamfain dillancin labaran Najeriya NAN ta bada rahoton cewa mabaracin na daya daga cikin masu bara shida da suka zauna kan titin jirgi a Mushin da safiyar Litinin.

Jirgin kasa ya murkushe mabaraci har lahira

Jirgin kasa ya murkushe mabaraci har lahira
Source: Depositphotos

Jerry Oche ya ce rayuwan kowani dan Najeriya na da muhimmanci amma mutane su bi doka da oda a daina zama kan hanyoyin wucewan jirgi.

Game da cewarsa, ya sabawa doka a gudanar da kasuwanci, zangon bara, ko wani aiki a bakin titin jirgi.

Yace: "Duk wanda bai da alaka da cikin jirgi kada ya zauna a gefe-gefen titin jirgi, saboda akwai hadari matuka. Tamkar kisan kai ganin jirgi na zuwa amma mutum ya zauna kan titin jirgi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel