Kamfanin Shell zai batar da Dala Biliyan 15 a cikin Najeriya - Darekta

Kamfanin Shell zai batar da Dala Biliyan 15 a cikin Najeriya - Darekta

Kamfanin nan na Shell Petroleum Development Company watau SPDC zai kashe kudi har fam Dala Biliyan 15 a Najeriya nan da shekaru 5 masu zuwa. Kwanan nan babban kamfanin ya bayyana wannan.

A karshen makon nan ne shugaban kamfanin Shell, Mista Osagie Okunbor, ya sanar da cewa za su kara karfin abin da su ka kashewa a Najeriya. Osagie Okunbor yace su na da shirin batar da Dala Biliyan 15 cikin shekaru 5 a kasar nan.

Okunbor yace wannan kudi da za su batar a Najeriya, zai taimaka sosai wajen samawa jama’an kasar aikin yi da kuma manyan kwangiloli. Tun ba yau ba dai wannan kamfani yake aiki tare da kuma taimakawa mutanen kasar.

KU KARANTA: Mataimakiyar Shugabar UN ta bayyana wanda zai mulki Najeriya a 2023

Babban Darektan wannan kamfanin mai na Najeriya, ya bayyana wannan ne a Ranar 7 ga Watan Afrilun nan a wajen wani taro na kungiyar NOGOF da hukumar kasar nan ta NCDMB ta shirya a cikin Garin Yenogoa a jihar Bayelsa.

Nan da shekaru 5 dai, wannan kamfani na da niyyar yin ayyuka kusan 30 a Najeriya wanda za a yi a cikin ruwa da tudu da kuma gangare domin ganin kowa ya amfana. Daga cikin wannan ayyuka akwai hakon rijiyoyi 2000 a cikin kasar.

Ba da dadewa bane wannan kamfani ya shigo da fam Dala Miliyan 300 cikin Najeriya domin wani aikin gas a jihar Imo. Idan an kamalla wannan aiki za a samu karuwar wutan lantarki da zai samawa gidaje fiye da miliyan guda wuta a jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel