Dalilin da yasa gwamnonin Najeriya basa zama a jahohinsu – Shehu Sani

Dalilin da yasa gwamnonin Najeriya basa zama a jahohinsu – Shehu Sani

Dan majalisa mai wakiltar al’ummar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani ya fallasa halin da yawancin gwamnonin Najeriya suke yin a waskewa daga jahohinsu su tare a babban birnin tarayya Abuja da sunan ganawa da shugaban kasa.

Sani ya bayyana haka ne a shafinsa na kafar sadarwar zamani na Twitter, inda yace gwamnonin sai su je su tare a Abuja, yayin da jahohinsu da jama’ansu suke cikin matsanancin tashin hankali na matsalar tsaro.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta dauki matasa dubu 130 a matsayin malaman gona

Dalilin da yasa gwamnonin Najeriya basa zama a jahohinsu – Shehu Sani

Shehu Sani
Source: Twitter

Legit.ng ta ruwaito Sanatan yana cewa gwamnonin suna fakewa ne da sunan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, a haka zasu kwashe tun daga litinin har Alhamis a Abuja, sai su shiga Villa a ranar Juma’a su yi sallah tare da shugaban kasa.

A wani kaulin kuma, Sanata Shehu Sani ya bayyana dalilin samun kashe kashe da rikice rikice a Najeriya, inda yace hakan ya samo asali ne tun lokacin da shuwagabannin Najeriya suka baiwa mulki fifiko fiye da jama’an da suke mulka.

“Masu rike da madafan iko sun fi fifita mulkinsu da ikonsu fiye da rayukan talakawa, don haka ba karamin hadari bane a dinga lallashin shuwagabanni a maimakon a tambayesu game da nauyin dake rataye a wuyansu.

“Kasa ta lalace idan har sai jama’a sun yi bore, sun nuna bacin ransu game da wata matsala kafin shuwagabanni su tashi tsaye wajen kare hakkin jama’ansu.” Inji Sanatan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel