Gobara ta tafka mummunan barna a jami’ar Umaru Musa Yar’adua

Gobara ta tafka mummunan barna a jami’ar Umaru Musa Yar’adua

Wata gobara da ta tashi a jami’ar tunawa da tsohon shugaban kasar Najeriya, kuma tsohon gwamnan jahar Katsina, Umaru Musa Yar’adua dake jahar Katsina ya haddasa mummunan barna a cibiyar ilimin.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gobarar ta taso ne da misalin karfe 10 na daren Litinin, 8 ga watan Afrilu inda a sashin ilimin kimiyyar Library and Information science na tsangayar Ilimi, inda ya kona ajin daukan darasi guda daya, ofishi, da kuma wani karamin dakin karatu.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta dauki matasa dubu 130 a matsayin malaman gona

Gobara ta tafka mummunan barna a jami’ar Umaru Musa Yar’adua

Gobara ta tafka mummunan barna a jami’ar Umaru Musa Yar’adua
Source: UGC

Sai dai duk da cewa ba ayi asarar rai a sanadiyyar gobarar ko samun rauni ba, amma an tafka asarar daruruwan takardun karatu daban daban, wanda hakan ya tilasta ma gwamnan jahar Katsina, Aminu Masari garzaya jami’ar don gane ma idanunsa.

Wani shaidan gani da, kuma dalibin jami’ar, Sani Ahmed ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace da ba don zuwan jami’an hukumar kashe gobara da Yansanda ba, da sashin ya kone kurmus gaba daya.

“Muna cikin dakunanmu sai muka hangi hayaki na fitowa daga ginin ya turnuke sama, nan da nan muka firfito, inda masu gadin jami’ar suka kira hukumar kashe gobara, anyi sa’a sun zo akan lokaci, ba da don haka ba da tsangayar ilimi gaba daya ya kone.” Inji shi.

A wani labari kuma majalisar gudanarwa ta jami’ar gwamnatin tarayya ta tunawa da tsohon Firai ministan Najeriya, Abubakar Tafawa Balewa dake jahar Bauchi, watau Abubakar Tafawa Balewa University, ATBU, ta sanar da nadin sabon shugaban jami’ar.

Majalisar ta sanar da sunan Farfesa Mohammed Abdulazeez a matsayin sabon shugaban jami’ar, watau Vice Chancellor, kamar yadda sakataren majalisar, Ahmed Hassan ya sanar a garin Bauchi a ranar Asabar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel