Babu rabuwar kai tsakanin Alkalai, Inji kotun koli

Babu rabuwar kai tsakanin Alkalai, Inji kotun koli

- Kotun koli na nan tsintsiya madaurinki daya

- Mai magana da yawun kotun yayi watsi rahotanni bogi kan raabuwar kan alkalai

Kotun koli ta kasa wato Supreme court ta bayyana cewa ajiye aiki da Alkalin alkalai na Najeriya Onnoghen yayi bai kawo rabuwar kawuna ba a tsakanin alkalai.

Majiyar Legit.ng ta sanar da cewa Onnoghen yayi murabus ne daga aikin nasa a ranar Alhamis awa 24 bayan Majalisar Alkalanci ta mika kudurinta na wannan bukata zuwa ga Shugaba Muhammadu Buhari bayan gudanar da bincike akan zargin da akeyi masa.

Justice Onnoghen

Justice Onnoghen
Source: UGC

KU KARANTA:Mataimakiyar shugaban majalisar dinkin Duniya ta bayyana wanda zai gaji Buhari a 2023

Rahoto da aka samu ranar Lahadi yayi ikirarin cewa aniyar Onnoghen tayin murabus ya kawo cece-kuce tsakanin ma’aikatan Kotun koli.

Amma zance daga bakin Daraktan labarai nata, Dr Festus Akande yayi watsi da wannan rahoto. Ga kuma abinda yake cewa, “Babu alamar kwayar zarra ta gaskiya cikin wannan zancen."

"Kotun koli ta Najeriya babbar cibiyace tamkar tsintsiya madaurinki daya wadda addini ko wani abu makamancin wannan baya kawo mata cikas.

Don haka yana da kyau jama’a su fahimci cewa babu ma’aikacin shari’a da ke aiki a bisa addininsa ko kabila wannan ya nuna babu wani bambanci a hanyarsu ta gudanar da ayyukansu.

Har kullum, Kotun kolin ta kasance mai gudanar da aiki ba tare da nuna bambancin addini kabila, ko yare ba kana tana aiki da hadin kai tsakanin ma’aikatanta don daga martabar wannan kotun.”

Dan asalin jihar Bauchi Mai shari’a Tanko Muhammad shine yake shugabantar wannan kotun a matakin rikon kwarya tun 23 ga watan Janairu bayan dakatarwar da Buhari yayi masa bisa ga dokar Code of Conduct Tribunal (CCT).

Haka zalika, Kungiyar Buhari ta fanni sadarwa ta ta caccaki jam’iyar PDP bisa ga kare Onnoghen da tayi akan dakatarwarsa.

Zance daga bakin Niyi Akinsiju (Coordinator) da Cassidy Madueke (Secretary) na kungiyar yace Buhari yayi abinda ya dace daidai kuma da kudurin kasa na dakatar da Onnoghen.

Ga abinda suke cewa, “Yan Najeriya sun ga yanda PDP tayi ta tsilla-tsilla tare da dan takararta Atiku Abubakar domin kare Onnoghen daga zargi gabanin zabe.

Jam’iyar ta PDP har dakatar da kamfe tayi tsawon awa 72 domin nuna rashin amincewarsu na dakatar da Alkalin suna ganin cewa haka zaluncine da kuma rashin adalci, sai dai kuma yan Najeriya sun san cewa zance nasu bashi da tushe balle mazauni.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel