Buba Galadima ya jawo wa ‘Diyar sa abin kunya – Inji Farfesa Sagay

Buba Galadima ya jawo wa ‘Diyar sa abin kunya – Inji Farfesa Sagay

Mun ji cewa shugaban kwamitin nan na PACAC da ke ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kan harkar yaki da rashin gaskiya watau Farfesa Itse Sagay, ya soki Hadimin Atiku, Buba Galadima.

Itse Sagay yayi hira jaridar Vanguard kamar yadda mu ka samu labari a farkon makon nan inda yayi watsi da maganar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi amfani da sojoji wajen murde babban zaben da aka yi a 2019.

Farfesan yake cewa ya rasa gane abin da yake damun Injiniya Buba Galadima, ganin yadda yake buga katabora a irin shekarunsa, Sagay yake cewa ‘Dan siyasar ya shiga wani hali da yake fadin abubuwan da sam ba su dace da shi ba.

Sagay yake cewa sojoji ba su murde zaben da aka yi a bana ba, illa ma dai yake cewa sun yi kokari ne wajen ganin an yi zabe cikin zaman lafiya a irin su Ribas da Akwa-Ibom. Sagay yace da a ce babu sojoji a jihohin, da an yi ta’adi.

KU KARANTA: Mace za ta gaji Shugaba Buhari a kan mulki a 2023

Buba Galadima ya jawo wa ‘Diyar sa abin kunya – Inji Farfesa Sagay

Sagay ya maidawa Buba Galadima martani game da ilmin diyarsa
Source: UGC

Farfesa Sagay ya nuna cewa dakarun sojoji sun taimaka ne wajen kade fitina a wadannan jihohi na Kudu da Zamfara da kuma yankin Boko Haram da aka tura su, akasin abin da jam'iyyar PDP ta saba na murde zabe a irin wannan jihohi.

Babban Masanin shari’ar ya kuma yi kaca-kaca da Galadima na cewa Diyarsa ta fi kowa ilmi a gwamnatin Buhari. Sagay yace hakan na nuna cewa gwamnatin shugaba Buhari tana aiki ne da cancanta wajen bada mukamai.

Lauyan yake nuna cewa Dattijon ‘dan siyasar ya jefa Diyar tasa cikin wani hali da ya zama dole ta rika jin kunyan baram-baramar Mahaifin ta. Har wa yau Sagay ya yabawa Buhari na kin sa hannu a kudirin da zai gyara harkar zaben kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel