Buhari zai bi kwararan matakai na ganin an daina kashe-kashen Zamfara

Buhari zai bi kwararan matakai na ganin an daina kashe-kashen Zamfara

A karshen makon jiya ne aka ji cewa Gwamnatin shugaba Muhammadu ta dakatar da duk wani aikin da ya shafi hako ma’adanan kasa a jihar Zamfara domin ganin kawo karshen kashe mutane da ake yi a wannan yanki.

Mun kawo maku jerin matakan da gwamnatin kasar ta dauka na ganin an samu zaman lafiya a jihar.

1. Dakatar da duk wani aikin hake-haken kayan arzikin kasa

Ba tare da wata-wata ba, daga Ranar Lahadi, 8 ga Watan Afrilu 2019, gwamnatin Najeriya ta haramtawa kowa cigaba da hake-haken ma’adanai a yankin Zamfara da jihohin kewaye masu arzikin gwal da wasu sinadarai a cikin kasa.

KU KARANTA: An kashe mutane da-dama a harin Kajuru a Jihar Kaduna

Buhari zai bi kwararan matakai na ganin an daina kashe-kashen Zamfara

Gwamnati na kokarin ganin an kawo karshen kashe rayuka a Zamfara
Source: Twitter

2. Hukunta wadanda su ka sabawa wannan doka ta gaggawa

Gwamnatin kasar tayi alkawarin damke duk wanda aka samu yayi kunnen kashi ya cigaba da aikin harko kayan alatun da ke karkashin kasa a wadannan yanki. Gwamnatin Najeriya za ta karbe lasisin wanda aka samu da wannan laifi har abada.

3. Fatattakar duk wani bako daga wadannan yankuna nan-take

Haka zalika gwamnatin kasar ta bada umarnin fatattakar duk wani wanda ya shiga irin wadannan yankuna a jihar Zamfara da nufin hako kayan arzikin kasa da ya tattara komatsan sa ya bar wuraren ba tare da wani ba lokaci ba domin a zauna lafiya.

Wannan matakai za su bada damar damke duk wasu masu tada kafar baya a yankin na Zamfara tare da rusa duk wata kafar ‘yan ta’adda. Wannan kuma zai bada damar dauke makaman da ake amfani da su, sannan kuma kasa za ta dawo hannun hukuma.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel