Gwamnatin Buhari ta dauki matasa dubu 130 a matsayin malaman gona

Gwamnatin Buhari ta dauki matasa dubu 130 a matsayin malaman gona

Gwamnatin tarayya ta dauki akalla matasa masu shaidar karatun kammala digiri su dubu dari da talatin, 130,000 a matsayin malaman gona ga manoman karkara, kamar yadda ministan harkar noma, Cif Audu Ogbeh ya bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ogbeh ya bayyana haka ne a yayin babban taron malaman gona na kasa karo na 24 daya gudana a babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Farfesa Mohammed: Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa ta samu sabon shugaba

A jawabinsa, Minista Ogbeh wanda ya samu wakilcin wata babbar daraktar ma’aikatan noma ta Najeriya, Karima Babangida, ya bayyana cewa gwamnati ta dauki matasan aikin ne a karkashin tsarin daukan aiki na N-Power.

Ministan yace akwai bukatar inganta sha’anin malaman gona domin cigaban harkar noma a Najeriya, musamman ta bangaren habbaka cinikin amfanin gona, ya kara da cewa a yanzu haka sun kammala horas da matasan, kuma za’a basu na’ura mai kwakwal don gudanar da aikinsu cikin sauki.

“Batun Ilimantar da manoma nada muhimmanci matuka ga cigaban noma a Najeriya, malaman noma suna bada gudunmuwa ga manoma tun daga wajen shuka, da kuma yadda ake amfani da injinoni a gona da kulawa dasu.” Inji shi.

Shima a nasa jawabin, shugaban kungiyar malaman gona ta Najeriya, Farfesa Lukman Akinbile ya bayyana cewa kungiyarsu na aiki kafada da kafada da sauran masu ruwa da tsaki wajen samar da dokokin da suka dace ga aikinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel