Buhari ya taikaita tafiyar sa, ya dawo daga Dubai

Buhari ya taikaita tafiyar sa, ya dawo daga Dubai

Da sanadin kamfanin dillancin labarai na Najeriya mun samu rahoton cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo kasar Najeriya daga birnin Dubai na Gabas ta Tsakiya a daren ranar Talata, 9 ga watan Afrilun 2019.

Buhari ya taikaita tafiyar sa, ya dawo daga Dubai

Buhari ya taikaita tafiyar sa, ya dawo daga Dubai
Source: Facebook

A yayin da aka kayyade tare da tsammanin dawowar shugaban kasa Buhari a ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu, rahotanni sun bayyana cewa ya yanke tafiyar sa da kwana guda inda ya sauka cikin birnin Abuja tun a daren Talata.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, jirgin shugaban kasa tare da tawagar sa ta hadimai da 'yan rakiya ya sauka a filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikwe da ke birnin Abuja da misalin karfe 10.45 na Yammaci.

Rahotanni sun bayyana cewa, akwai yiwuwar shugaban kasa Buhari ya takaice tafiyar sa domin gaggauta dawowa wajen tunkarar kalubale na rashin tsaro da ya mamaye jihar Zamfara, Kaduna da kuma wasu sassan kasar nan.

KARANTA KUMA: Zan kara tsananta yaki da rashawa da habaka tattalin arziki - Buhari

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari a ranar 4 ga watan Afrilu ya shilla zuwa kasar Jordan domin amsa goron gayyata na Sarkin Jordan, Mai Martaba Abdullah II bin Al-Hussein wajen halartar taron tattalin arziki na duniya.

Shugaban kasa Buhari a ranar Lahadi ya kuma kutsa birnin Dubai inda ya halarci taron zuba hannun jaro karo na 9. Ya kuma gana da kungiyoyin hannun jari daban-daban tare da aiwatar da zaman sauraron ra'ayin al'ummar Najeriya mazauna Dubai.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel