Dalilin da ya sa na sauka daga kujera ta a 2015 - Jonathan

Dalilin da ya sa na sauka daga kujera ta a 2015 - Jonathan

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Dakta Goodluck Ebele Jonathan, ya ce kyautata zato ga makomar dimokuradiyya a nahiyyar Afirka ya sanya ya hakura ya mikawa shugaba Muhammadu Buhari akalar jagoranci a 2015.

Domin kyautata makomar dimokuradiyya a nahiyyar a Afirka baki daya, ya sanya a shekarar 2015 tsohon shugaban kasar Jonathan ya sadaukar da kudirin sa wajen hakura da jagorancin kasar a karo na biyu.

Dalilin da ya sa na sauka daga kujerar ta a 2015 - Jonathan

Dalilin da ya sa na sauka daga kujerar ta a 2015 - Jonathan
Source: Depositphotos

Tsohon shugaban kasa Jonathan da ya kasancewa babban bako na musamman ya bayyana hakan yayin gabatar da jawaban sa a taron karawa juna sani kan al'amurran da su ka shafi harkokin zaben kasa da aka gudanar cikin garin Abuja a ranar Talata.

Jonathan wanda hadimin sa ya wakilta yayin taron, Nze Akachukwu Nwankpo, ya ce ya sadaukar da kudirin sa na ci gaba da jagorancin kasar nan domin tabbatar da kyakkyawar makomar dimokuradiyya a nahiyyar Afirka.

KARANTA KUMA: Buhari ya taikaita tafiyar sa, ya dawo daga Dubai

Ya yabawa abokanan arziki da kuma kungiyoyi masu fafutikar kare hakkin dan Adam da su ka dauki nauyin shirya wannan taro domin tunawa da akidun marigayi Oronto Douglas, tsohon hadimin sa a kan harkokin da su ka shafi Neja Delta, da ya riga mu gidan gaskiya a 2015.

Cikin na sa jawaban, tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ken Nnamani, ya yi babatu tar da kausasa harshe dangane da tabarbarewa harkokin zabe. Ya ce kuri'u sun dai na tasiri wajen rinjayar da sakamakon zaben kasar nan a halin yanzu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel