Zan kara tsananta yaki da rashawa da habaka tattalin arziki - Buhari

Zan kara tsananta yaki da rashawa da habaka tattalin arziki - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talatar da ta gabata ya sha alwashin sake zage dantsen sa wajen tsananta yaki da rashawa, habaka tattalin arziki da kuma kawo karshen ta'addanci a wa'adin sa na biyu.

Zan kara tsananta yaki da rashawa da habaka tattalin arziki - Buhari

Zan kara tsananta yaki da rashawa da habaka tattalin arziki - Buhari
Source: Facebook

Shugaban kasa Buhari yayin ganawa da al'ummar Najeriya mazauna kasar Dubai a ranar Talata, ya sake sabunta alkawalin sa na tsananta yaki da rashawa da kuma kara kaimi wajen yakar ta'addanci cikin tsawon shekaru hudu masu zuwa a gwamnatin sa.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari cikin lasar tsinin takobi ya ce tattalin arzikin kasar nan zai habaka tare da taka matakin na inganci gabanin saukar sa daga kujerar mulki a 2023.

Shugaban kasar ya gudanar da wani zaman sauraron ra'ayi da al'ummar Najeriya a kasar Dubai inda ya shaida masu yadda gwamnatin sa za ta yi tattalin albarkatun kasa domin bunkasa tattalin arziki tare da bayar da mafificin muhimmanci a kan harkokin noma.

KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun hallaka Mutane 21 a Kaduna

Kakakin shugaban kasa Femi Adesina, ya ce shugaba Buhari cikin jawaban sa ya bayar da shaidar yadda akidar sa ta mataki na gaba wato Next Level, ke da manufa ta jajircewa wajen bunkasa kwazon gwamnatin sa gabanin 2023 fiye da yadda ta kasance a tsakanin 2015 zuwa 2019.

Yayin hikaito yadda gwamnatin sa ta samu nasarorin gaske wajen yakar ta'addanci musamman durkusar da kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas, ya yi kira na neman al'ummar Najeriya su daura damarar riko da noma da ta kasance tushe na arziki.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel