'Yan bindiga sun hallaka Mutane 21 a Kaduna

'Yan bindiga sun hallaka Mutane 21 a Kaduna

Kimanin rayukan Mutane 21 sun salwanta yayin aukuwar wani mummunan hari na 'yan bindiga a kan al'ummomin Banono da kuma Anguwan Aku da ke gundumar Kufana karkashin karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, harin ya auku ne da misalin karfe 9.30 na safiyar ranar Litinin inda 'yan ta'addan haye kan Baburan su ke ci karen su ba bu babbaka a kauyukan Banono da kuma Anguwan Aku na gundumar Kufana da ke karamar hukumar Kajuru.

'Yan bindiga sun hallaka Mutane 21 a Kaduna

'Yan bindiga sun hallaka Mutane 21 a Kaduna
Source: UGC

Yayin tabbatar da aukuwar harin, kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, DSP Yakubu Sabo ya bayyana cewa, maharan rike da bindigu bayan sace kimanin shanu 50 da hallaka Mutane 3, sun kuma kone gidaje 10 a yankunan al'ummomin biyu.

Rahotanni sun bayyana cewa, hadin gwiwar jami'an tsaro na dakarun soji da kuma 'yan sanda ta yi tasiri wajen dakile kaifin harin yayin da suka garzaya da wadanda su ka raunata zuwa asibiti gami da kwantar da tarzoma.

Majiyar jaridar Legit.ng yayin kididdigar ta'asar da ta'addanci masu ta'adar ya harin haifar ta ruwaito cewa, rayukan mutane 21 sun salwanta, Mutane 3 sun jikkata, gidaje 10 sun kone kurmus gami da satar shanu kimanin hamsin.

KARANTA KUMA: Buhari ya dauki nauyin jan ragamar kawo karshen ta'addanci a Najeriya - Sufeton 'Yan sanda

Kakakin 'yan sanda ya bayyana cewa, a halin yanzu dakarun tsaro sun matsa bincike domin bankado miyagun da ke da hannu cikin wannan mummunar aika-aika da tayi tasiri wajen tayar da hankulan al'umma ba bu shiri.

Kazalika DSP Sabo ya bayyana yadda damuwar kwamishinan 'yan sanda na jihar, Ahmad Abdurrahman, inda ya lashi takobi na daurin damarar damko miyagun da su zartar da wannan mummunan ta'addanci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel